Ana Murnar Ceto Daliban Maga, 'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Hukumar NIS a Kebbi
- Ana zargin ’yan kungiyar ta’addanci ta Lakurawa da kai hari kan jami'an hukumar NIS a yankin karamar hukumar Bagudo a Kebbi
- Wannan hari na zuwa ne kwanaki kadan bayan an yi nasarar ceto daliban makarantar mata ta Maga da aka sace kwanakin baya
- Rahoto ya nuna cewa ’yan bindigar sun bude wa jami’an NIS wuta da tsakar dare, suka kashe uku da ke bakin aiki nan take
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Wasu ’yan bindiga da ake zargin mambobin kungiyar ta’addanci ta Lakurawa ne sun kai wa jami'an hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) hari a jihar Kebbi.
'Yan ta'addan dauke da miyagun bindigogi sun kai farmaki wani shingen bincike na jami'an NIS da ke Bakin Ruwa, kusa da kan iyakar Maje da ke cikin Karamar Hukumar Bagudo.

Source: Twitter
An kashe jami'an NIS 3 a Kebbi
Jaridar Leadership ta tattaro cewa maharan sun tafka barna a harin, inda suka hallaka jami'an hukumar guda uku nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin, wanda ya faru kusan ƙarfe 1:00 na tsakar dare a ranar Alhamis, ya jefa mazauna yankin cikin tsoro da tashin hankali, musamman mutanen da ke zaune a kusa da iyakar Najeriya da Benin.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Channels TV cewa ’yan bindigar sun isa wurin ba zato ba tsammani, suka tarwatsa mutane kana suka bude wuta kan jami’an da ke bakin aiki, inda suka kashe su nan take.
Wani majiya ta tsaro ya ce maharan sun gudu ta cikin dazuzzuka da ke kusa bayan kai farmakin.
Wane mataki hukumomi suka dauka?
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kebbi, Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu ba su samu cikakken bayani kan harin ba, domin jami’an tsaro na kokarin tattara rahotanni.
Sai dai duk wani yunkuri na jin ta bakin hukumar NIS ya ci tura, domin jami'in hulda da jama'a na hukumar reshen jihar Kebbi bai daga kiran wayar da aka masa ba.
Amma wasu mazauna yankin da kuma jami’ai na wasu hukumomin tsaro tsaro da ke Bagudo, da suka nemi a sakaya sunayensu, sun tabbatar da harin.
Majiyoyi sun tunatar da cewa kimanin makonni uku da suka gabata, mahara sun kashe jami’in hukumar Kwastam a yankin.
Wani da ya tsira daga harin ya ce:
“Sun zo da yawa, suna ta harbi ba kakkautawa. Mutane suka tarwatse domin ceton rayukansu."

Source: Original
An dade ana danganta kungiyar Lakurawa da kai hare-hare, kisan jama’a da kuma kai farmaki kan jami’an tsaro a sassan Jihar Kebbi.
Hukumomin tsaro sun ce ba su kai ga gano dalilin da ya sa aka kai wannan hari ba tukuna, amma bincike na ci gaba.
Gwamnan Kebbi ya ja hankalin daliban Maga
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya bada shawara ga ’yan mata 24 da aka ceto na makarantar sakandaren mata ta GGCSS Maga.

Kara karanta wannan
Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada
Da yake jan hankalin daliban kafin mika su ga iyayensu, Gwamna Nasir ya bukaci 'yan matan da su birne abin da ya faru, kada au bari ya hana su ci gaba da neman ilimi.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa iyayen yaran cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace don tallafa wa ’ya’yansu su ci gaba da karatu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

