Daga Cacar Baki, Matasa Sun Caccaka wa Babban Dan Sanda Wuka, Ya Sheka Lahira
- 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar daya daga cikin jami'anta da ke bakin aiki bayan harin da matasa 'yan daba suka kai masa
- 'Dan sandan ya rasu bayan hatsaniya da ta barke a tsakaninsu wanda ya jawo masa munanan raunuka da suka yi ajalinsa
- Rundunar ‘yan sanda ta ce an kama mutum biyu da ake zargi, yayin da ake ci gaba da bincike kan kisan jami’in
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - An kashe wani jami’in ‘yan sanda da yake kan aiki bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun caka masa wuka a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Majiyoyi sun ce an farmake shi ne a kusa da yankin Arakale bayan wata takaddama da ta tashi tsakaninsa da wadanda suka kai harin.

Source: Facebook
Yadda miyagu suka cakawa dan sanda wuka
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, Olushola Ayanlade ya tabbatar da lamarin a jiya Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayanlade ya ce abin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, sabanin jita-jitar da ke yawo cewa da yammaci abin ya faru.
Kakakin rundunar yan sanda ya bayyana cewa jami’in yana cikin aikin sintiri ne da sassafe lokacin da ya hadu da wasu mutane masu halin banza da tayar da rigima.
Ya ce:
“Abin da ya fara da tattaunawa ta yau da kullum ya rikide ya koma tashin hankali. Daya daga cikin maharan ya soki jami’in, lamarin da ya jefa shi cikin mummunan hali. Nan take aka dauke shi zuwa asibiti domin kulawar gaggawa.”
Ya ce an aika karin jami’an tsaro wurin don dawo da doka da oda tare da kama wadanda ake zargi.

Source: Original
Nasarar da yan sanda suka samu
An kama mutane biyu, Shina Jacob, mai shekara 25, da Felix Olalekan, mai shekara 32, bisa alaƙa da faruwar lamarin.
An garzaya da jami’in asibiti domin ceto rayuwarsa, amma ya rasu duk da irin kokarin da aka yi don cetonsa, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.
Ya kara da cewa bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala binciken.
Haka kuma, ya yi gargadi kan yada labaran ƙarya da ka iya tayar da tsoro ko rikitar da jama’a game da gaskiyar abin da ya faru.
Wasu majiyoyi sun ce cikin wadanda ake zargi akwai yaran gwamna wanda daya daga cikinsu ma gwamnan Ondo da kansa ya ba shi mukami a gwamnati a watan Satumbar 2025.
An cakawa jami'ar NSCDC wuka a Abuja
An ji cewa wasu bata-gari sun cakawa wata jami’ar NSCDC, Akpan Blessing wuka a kofar gidanta da ke Abuja, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.
An ce an kai ta asibitoci daban daban amma ba a karɓe ta ba saboda babu rahoton ‘yan sanda, abin da ya sa ta zubar da jini har ta mutu.
Rahoto ya nuna cewa wasu asibitocin sun ki karɓar ta duk da an nuna masu katin aikinta, yayin da rundunar ta yi shiru kan lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


