Trump: Tinubu Ya Zakulo 'Yan Najeriya da Za Su Yi Aiki da Amurka kan Tsaro

Trump: Tinubu Ya Zakulo 'Yan Najeriya da Za Su Yi Aiki da Amurka kan Tsaro

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa tawagar Najeriya da za ta shiga kwamitin hadin guiwar tsaro tsakanin kasar da Amurka
  • Tawagar za ta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a ziyarar da manyan jami’an tsaro na Najeriya suka kai Washington DC
  • Sabon tsarin ya samo asali ne bayan barazanar Donald Trump na aika sojojin Amurka zuwa Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa tawagar Najeriya wacce za ta wakilci kasar a sabon kwamitin hadin gwiwa na tsaro da Amurka.

An kafa kwamitin ne domin karfafa dangantaka a fannin yaki da ta’addanci da musayar bayanan sirri.

Shugabannin Najeriya da Amurka
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa kwamitin na daga cikin manyan sakamakon ganawar da aka gudanar makon jiya a Washington DC.

Kara karanta wannan

Maganganun Sanata sun tada kura yayin wata muhawara mai zafi a Majalisar Dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda Tinubu ya nada su wakilci Najeriya

Punch ta rahoto cewa shugaba Tinubu ya nada Nuhu Ribadu a matsayin shugaban tawagar Najeriya a kwamitin hadin gwiwar.

Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce:

“Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa tawagar Najeriya a kwamitin hadin gwiwar tsaro na Amurka da Najeriya, a wani mataki na zurfafa aiki tare wajen shawo kan matsalolin tsaro.”

Kwamitin zai samu goyon bayan manyan jami’an gwamnati da na tsaro, ciki har da Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar.

Mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu
Nuhu Ribadu da ke ba Bola Tinubu shawara kan tsaro. Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Twitter

Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar; ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo; da Ministan harkokin jin kai, Dr Bernard Doro na cikin tawagar Najeriya.

Haka kuma tawagar ta kunshi babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Mohammed Mohammed; da Sufeton ’yan sanda, Kayode Egbetokun.

Don tabbatar da daidaito tsakanin Abuja da Washington, an nada Idayat Hassan daga ONSA da Paul Alabi daga ofishin jakadancin Najeriya a Amurka a matsayin sakatarorin kwamitin.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Amurka ta yi wa Najeriya kan matsalar rashin tsaro

Burin Najeriya/Amurka a sabon tsarin tsaro

Wani rahoto ya ce shugaba Tinubu ya umarci mambobin tawagar da su yi aiki kafada da kafada da takwarorinsu na Amurka domin aiwatar da duk yarjejeniyoyin da aka cimma a ziyarar makon jiya.

Najeriya da Amurka sun kara dangantakar tsaro a cikin sama da shekaru 10 da suka gabata, musamman wajen yaki da ta’addanci, kare iyakoki da yaki da garkuwa da mutane.

Sai dai gwamnatin Tinubu na neman tsarin da zai taimaka domin shawo kan barazanar ta’addanci, ’yan bindiga, safarar makamai da sauran manyan laifuffuka.

Sabon tsarin ya biyo bayan barazanar shugaba Donald Trump, wanda ya yi ikirarin cewa zai iya tura sojojin Amurka zuwa Najeriya da bindigogi.

Harin dan bindiga ya kashe sojar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wata sojar Amurka mai suna Sarah Beckstrom ta rasu bayan harin da wani dan bindiga ya kai musu.

Wani dan bindiga ne ya budewa sojojin kasar wuta a kusa da fadar shugaban Amurka ta White House.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Bola Tinubu ya dauka bayan sace dalibai a Kebbi da Neja

Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna matukar damuwa game da mutuwar sojar yana mai cewa zai dauki matakai masu tsauri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng