Sojar Amurka Ta Rasu bayan Harin da Dan Bindiga Ya Kai Musu, Trump Ya Fusata
- Wata sojar Amurka ta rasu, yayin da wata kuma ke cikin mawuyacin hali bayan harin da aka kai musu a Washington DC
- Hukumomi sun ce wanda ake zargi, Rahmanullah Lakanwal daga kasar Afghanistan, ya jikkata lokacin cafke shi
- Lamarin ya sa Donald Trump ya sake kira da tsaurara dokokin shige-da-fice, har da dakatar da shigowar 'yan wasu kasashe
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – An shiga jimami a ƙasar Amurka bayan mutuwar wata soja 'yar jihar West Virginia, Sarah Beckstrom da aka harba a Washington DC.
A wata sanarwa, rundunar sojojin Amurka ta tabbatar da cewa wata sojar da ke tare da ita tana fama da jinya a asibiti bayan harin da ake zargin an kai musu da gangan.

Source: Twitter
Rahotanni daga CNN sun nuna cewa wanda ake zargi, Rahmanullah Lakanwal dan Afghanistan, ya jikkata lokacin da jami’an tsaro suka kama shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan harin, hukumomin Amurka sun ce ana sake duba batutuwan neman mafaka, katin zama dan kasa, da kuma yiwuwar korar iyalan wanda ake zargi idan bincike ya tabbatar da hakan.
Martanin Trump kan mutuwar sojar Amurka
Lamari ya tayar da hankali, inda Shugaba Donald Trump ya yi kira da a dauki matakan shige-da-fice mafi tsauri
Rahoton New York Times ya ce Trump ya ce:
“Zan dakatar da shigowar baki daga dukkan kananan kasashe domin tsarin Amurka ya samu damar murmurewa gaba ɗaya.”
Ya ce gwamnati za ta kawo ƙarshen abin da ya kira “shigowar bakin haure da gwamnatin Biden ta bari,” tare da cewa duk wanda ba ya da “fa’ida ga Amurka” ko “ba ya son ƙasar” za a mayar da shi.
Ba a fayyace ƙasashen da yake nufi ba, sai dai wannan nau’in magana na cikin kalaman da yake amfani da su wajen adawa da shige-da-fice.
Wace ce sojar, Amurka Sarah Beckstrom?
Rundunar sojojin Amurka ta jihar West Virginia ta tabbatar da mutuwar Sarah Beckstrom, wadda ta kasance sojar Amurka mai shekaru 20.
Ta shiga rundunar ne a ranar 26, Yuni, 2023, tana aiki a matsayin jami’a mai bayar da tsaro ga al'ummar kasar.
A cewar rundunar, Sarah ta yi aikin sintiri a babban birnin Amurka a karkashin shirin Operation DC Safe and Beautiful.
Fadar White House ta bayyana cewa Shugaba Trump ya tuntubi iyayenta domin yi musu ta’aziyya, yana mai cewa:
“Ta kasance abin misali a dukkan fannoni.”
A wani taron godiya ga jami’an tsaro, ya sake cewa:
“Ta kasance mai kokari matuka, kuma na ji ana yaba mata sosai.”
Da aka tambaye shi ko zai halarci jana’izarta, Trump ya ce bai yanke shawara ba tukuna, amma “za ta iya yiwuwa,” yana mai cewa yana kaunar jihar West Virginia.

Source: Getty Images
'Dan bindigan da ya harbi sojojin Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Amurka ta fitar da bayanai game da wani dan bindiga da ya harbi sojojin kasar.
Ma'aikatar harkokin gidan Amurka ta bayyana cewa wanda ake zargi da kai harin shi ne Rahmanullah Lakanwal daga Afghanistan.
Donald Trump ya yi Allah wadai da harbin sojojin da aka yi, yana mai cewa Joe Biden ne ya ba 'yan kasarsa damar shiga Amurka a baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


