Yadda Jikin Shehu Dahiru Bauchi Ya Yi Tsanani, aka Tafi da Shi Asibiti Ya Rasu

Yadda Jikin Shehu Dahiru Bauchi Ya Yi Tsanani, aka Tafi da Shi Asibiti Ya Rasu

  • Shahararren malamin addinin Musulunci kuma jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu yana da shekaru 98
  • Iyalan marigayin sun tabbatar da cewa za a yi jana’izarsa yau bayan sallar Juma’a a gidansa da ke Unguwar Jaki a garin Bauchi
  • Sakataren babban malamin, Malam Baba Ahmad ya bayyana yadda jikin marigayin ya yi tsanani kuma aka tafi da shi asibiti ya rasu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – An shiga jimami a fadin Najeriya bayan rasuwar malamin addinin Musulunci kuma jagoran darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, ya fadi alherin da ya yi masa

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya rasu a daren Alhamis da misalin ƙarfe 1:30 bayan rashin lafiya.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shehu Dahiru Usman Bauchi a shekarun baya. Hoto: Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta fitar da wani rahoto na musamma game da abubuwan da suka faru a karshen rayuwar marigayin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakatarensa, Malam Baba Ahmad, ya tabbatar da cewa marigayin ya ci abinci a daren da ya rasu kafin jikinsa ya sauya.

Yadda Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu

Bayanai daga bakin sakatarensa sun nuna cewa marigayin yana cikin iyalansa kafin yanayin lafiyarsa ya sauya a ranar Laraba da daddare.

Bayan cin abincin dare da misalin ƙarfe 8:00 na yamma, Baba Ahmad ya ce sun tattauna da shi na ɗan lokaci, sai kuma jikinsa ya sauya kwatsam.

A wannan lokaci aka garzaya da shi asibitin koyarwa na ATBU, inda likitoci suka yi iya ƙoƙarinsu don farfaɗo da shi kafin daga bisani ya riga mu gidan gaskiya da misalin ƙarfe 1:30 na dare.

Baba Ahmad ya bayyana cewa marigayin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar addini ta hanyar wa’azi, karantarwa da taimakon marasa galihu.

Kara karanta wannan

Sheikh Sharif Saleh zai yi wa marigayi Dahiru Usman Bauchi sallar jana'iza

Ya ce:

“Mun rasa uba, jagora kuma uban-gida mai matuƙar tausayi da halin kirki. Alhamdulillah, ya bar tarihi da za a ci gaba da tunawa da shi.”

Dahiru Bauchi: An tuntubi Sharif Saleh kan jana'iza

A cikin bayanan da aka samu daga iyalansa, ɗansa Ahmad Tijjani Dahiru Bauchi ya ce za a yi sallar jana’iza bayan sallar Juma’a.

Ya bayyana cewa marigayin ya dade yana bayyana burinsa na a birne shi kusa da kabarin ɗansa, Dr Hadi Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar 5, Disamba, 2005.

Sheikh Sharif Saleh da Dahiru Bauchi
Dahiru Bauchi, dan shi da Sheikh Sharif Saleh. Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Iyalan marigayin sun tabbatar da cewa an tuntubi Sheikh Sharif Saleh Maiduguri kuma ya amince da zai kasance a jihar Bauchi domin sallar jana'izar.

Ana sa ran jana'izar malamin za ta hada manyan mutane a ciki da wajen Najeriya saboda yadda ya sanu a kasar, Afrika da ma fadin duniya.

Dikko Radda ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

Kara karanta wannan

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta girgiza Sanata Barau, ya fadi yadda ya ji

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin jihar Katsina ta ce ta shiga damuwa game da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana wasu ayyukan da ya ce marigayin ya yi a lokacin rayuwarsa da za a tuna shi da su.

Ya kuma mika sakon jaje ga gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da dukkan iyalan marigayin bisa rashin da suka yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng