'Yan Ta'adda Sun Farmaki Tawagar Tsohon Ministan Najeriya, An Samu Asarar Rayuka
- ‘Yan bindiga sun kai hari kan ayarin tsohon ministan kwadago, kuma tsohon gwamnan Anambra, Dr. Chris Ngige
- Maharan sanye da kayan soja da ‘yan sanda sun bude wuta kan motar jami'an tsaro, suka kashe dan sanda, suka sace bindigarsa
- An ce 'yan bindigan sun kuma harbe wata mata har lahira a lokacin da take kokarin nadar bidiyon wannan hari a wayarta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Tashin hankali ya sake mamaye yankin Nkpor–Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa, jihar Anambra, yayin da aka kai wa tawagar Chris Ngige hari.
An rahoto cewa wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan ayarin tsohon gwamnan Anambra, Dr. Chris Ngige, a safiyar Laraba.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun farmaki tawagar tsohon minista
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun iso sanye da kayan jami’an tsaro – wasu cikin kayan soja, wasu cikin kayan ‘yan sanda.
An ce wannan batar da kama da miyagun suka yi ya sanya jama’a suka kasa gane su kafin su bude wuta a kan motar jami'ai da ke rakiyar ayarin.
An kashe dan sanda, an dauke bindigarsa
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’in dan sanda da ke cikin motar rakiyar ya mutu nan take, sannan maharan suka sace bindigarsa da kayan aikinsa.
An kuma rahoto cewa motar ta yi kaca-kaca da harsasai, abin da ke nuna karfin bindigogin da 'yan ta'addar suka yi amfani da su.
Wata mata da aka ce tana kokarin daukar bidiyon harin da wayarta, ita ma maharan suka harbe ta har lahira, in ji rahoton The Sun.
Wani mai shago da ya fito da gaggawa don ganin abin da ke faruwa ya sha harbin harsasai, lamarin da ya sa ya yi asarar jini mai yawa.
Amma rahoto ya nuna cewa likitoci sun ce an riga sun shirya yin masa tiyata don cire harsasai daga jikinsa da kuma kokarin ceto rayuwarsa.

Source: Facebook
Tsohon minista ya yi martani kan harin
Shugaban rundunar tsaron da ke raka ayarin Ngige ya ji munanan raunuka, amma tuni aka yi masa tiyata a asibiti. Likitoci sun tabbatar da cewa yana murmurewa sannu a hankali.
Rahoto ya nuna cewa Dr. Ngige dai ba ya cikin ayarin a lokacin da harin ya auku, lamarin da ya ceci rayuwarsa.
A wata sanarwa da tsohon sakataren yada labaransa, Fred Chukwuelobe, ya fitar, an tabbatar da faruwar lamarin tare da bayanin cewa Ngige ya samu cikakken bayani daga tawagarsa.
“Na yi magana da Dr. Ngige kai tsaye, ya tabbatar da harin. Ya kuma tabbatar da cewa ana kula da wadanda suka jikkata yadda ya kamata."
- Fred Chukwuelobe.
Hukumar ICPC ta titsiye Chris Ngige
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Chris Ngige, tsohon ministan kwadago ya gurfana gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.
Hukumar ICPC ta titsiye Ngige kan zargin ya taka rawa a badakalar kwangiloli da kuma ta daukar ayyuka a lokacin ya ke kan kujerar minista.

Kara karanta wannan
An kashe mutum 2 da ƴan bindiga suka je sace dalibai a Kogi? Gwamnati ta yi martani
Tsohon ministan ya kasance a gaban jami’an ICPC na tsawon sa’o’i biyar yana amsa tambayoyi kan kwangilolin da aka ba NSITF lokacin shugabancinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

