Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Bude wa Dakarun Ƴan Sanda Wuta, Sun Tafka Barna

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Bude wa Dakarun Ƴan Sanda Wuta, Sun Tafka Barna

  • 'Yan bindiga sun bude wuta kan tawagar sintiri ta rundunar 'yan sanda a Anambra inda aka yi musayar wuta mai zafi
  • An rahoto cewa maharan sun zo cikin motoci uku, sanye da kayan jami'an tsaro, kuma suna dauke da miyagun makamai
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da harin, yayin da ta roki jama'a su rika taimakawa jami'ai da rahoton abubuwan da ke faruwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai farmaki kan tawagar sintiri ta jami'an rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra.

An rahoto cewa 'yan ta'addar sun farmaki 'yan sandan ne lokacin da suke sintiri a kan hanyar Abatete–Eziowelle da ke Idemili ta Arewa.

'Yan bindiga sun farmaki jami'an 'yan sanda da ke aikin sintiri a jihar Anambra.
Jami'an rundunar 'yan sanda suna sintiri a kan tituna. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Anambra

Kara karanta wannan

Bincike: Ƴan sanda sun bayyana wadanda ake zargi da sace mutane 10 a jihar Kwara

Jaridar Punch ta rahoto cewa an samu musayar wuta mai tsanani tsakanin 'yan sanda da 'yan bindigar, lamarin da ya jefa al'ummar yankin a tashin hankali.

Rahoton ya nuna cewa wani dan sanda ya samu rauni, sannan an ƙona motar da 'yan sanda ke sintiri da ita yayin wannan artabu.

Maharan sun kaddamar da harin ne dauke da miyagun makamai, kuma majiyoyi sun ce miyagun sun kai hari a wasu motoci marasa lamba.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun yi wa jami’an ‘yan sanda kwantan ɓauna yayin da tawagar DOPS da ta yaki da kungiyoyin asiri ke sintiri.

Abin da majiyoyi suka ce kan harin Anambra

Wani shaidan gani da ido ya rahoto cewa:

“Sun zo cikin motoci uku: Farar Toyota bas, baƙar Lexus 350 kirar SUV, da farar Toyota Highlander, dukkansu ba su da lamba. Kuma suna sanye da kayan jami'an tsaro."

A cewar majiyar, maharan sun bude wuta kan 'yan sandan ba kakkautawa, inda su ma jami'an suka mayar da martani, wanda ya jawo musayar wuta ta dogon lokaci.

Kara karanta wannan

Bayan sace 'yan mata a Borno, 'yan ta'addan ISWAP sun kinkimo batun kudin fansa

Zagazola Makama ya rahoto a shafinsa na X cewa, motar sintirin SPACS ta kama da wuta bayan ta sha ruwan alburusai yayin da wata motar DOPS ita ma ta lalace saboda harbin da ta sha.

Duk da haka, jami’an ‘yan sandan sun yi nasarar fatattakar maharan, amma an rahoto cewa ɗaya daga cikinsu ya samu rauni.

An rahoto cewa musayar wuta mai zafi da aka yi tsakanin 'yan bindiga da 'yan sanda ta jawo lalacewar motocin sintiri a Anambra.
Taswirar jihar Anambra, inda 'yan bindiga suka yi wa 'yan sanda kwanton bauna. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Martanin rundunar ‘yan sandan Anambra

Kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, inda ya ce maharan sun farmaki jami’an ne amma aka yi nasarar dakile harin.

Ya ce:

“Rundunar ta fatattaki maharan. Babu wani farar hula da ya ji rauni. Kwamishinan ‘yan sanda ya ba da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a fadin jihar.”

SP Tochukwu Ikenga ya roki jama’a su kwantar da hankulansu, su kuma rika kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ba su yarda da shi ba.

'Yan bindiga sun shiga Anambra sun bude wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu asarar rayuka da dama da wasu yan bindiga suka bude wuta kan al'umma a wani kauye da ke jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Tsohon minista: 'Abin da ya sa 'yan bindiga ke garkuwa da yara 'yan makaranta'

Lamarin ya faru ne a kusa da kasuwar Nwochichi da ke karamar hukumar akwa ta Kudu, inda da miyagun suka fito a cikin mota kirar Jeep suka fara sakin wuta.

Kakakin yan sanda a jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya fadi matakin da suka dauka bayan wannan hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com