Abin da Malam Kabiru Gombe Ya Ce bayan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Abin da Malam Kabiru Gombe Ya Ce bayan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

  • Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana alhini game da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda ya tura sakon ta’aziyya ga al’ummar Musulmi
  • A cikin sanarwar da ya wallafa a kafar sadarwa, ya jajanta wa dangin Shehu Dahiru Bauchi, yana mai cewa rasuwar ta yi matuƙar girgiza al’umma
  • Sheikh Gombe ya roƙi Allah ya gafarta wa marigayin, ya ƙara masa rahama, sannan ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi da ya shafi kowa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Kamar sauran malaman Musulunci a Najeriya, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ta tura sakon ta'aziyya ga al'ummar Musulmi.

Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a yau Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025 da muke ciki.

Kabiru Gombe ya tura sakon ta'aziyya bisa rasuwar Dahiru Bauchi
Marigayi Dahiru Bauchi da Sheikh Kabiru Gombe. Hoto: Muhammad Kabir Haruna.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin yau Alhamis 27 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya yi nasiiha mai ratsa zuciya kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Bauchi ta jajanta rasuwar Dahiru Bauchi

Hakan na zuwa ne bayan fitar da sanarwar ta'aziyya da gwamnatin jihar Bauchi ta yi game da rasuwar dattijon da ya ba da gudunmawa ga al'ummar Musulmi baki daya.

Gwamna Bala Mohammed ya aika da sakon ta’aziyya a madadin gwamnatin Bauchi zuwa ga iyalansa, almajiransa da Musulmin duniya.

Ya ce marigayin babban malami ne da ya shahara wajen koyar da Alkur'ani, kuma ya ba da gudunmawa ga ilimin addinin Musulunci.

Bala Mohammed ya yi jimamin rasuwar Dahiru Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: Senator Bala Abdullahi Mohammed.
Source: Twitter

Dahiru Bauchi: Abin da Kabiru Gombe ya ce

A cikin rubutunsa, Kabiru Gombe ya tura sakon ta'aziyya na musamman ga iyalan marigayin da yan uwa da abokan arziki.

Ya yi addu'a ga marigayin domin samun rahama a gobe kiyama tare da ba iyalansa hakuri na jure wannan rashi.

Kabiru Gombe ya ce:

"InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un.
"Ina miƙa ta'aziyya ga ƴan uwa da iyalan Shehu Ɗahiru Bauchi da al-ummar jihar Bauchi dama ƙasa baki ɗaya, bisa rasuwar Shehu Ɗahiru Usman Bauchi.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izala ta yi magana, ta tura sako ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi

"Allah ka gafarta masa kura-kuransa, ka baiwa iyalansa dangana."

Martanin al'umma bayan ta'aziyyar Kabiru Gombe

Mutane da dama sun yi martani bayan rubutun Malam Kabiru Gombe game da jajantawa iyalan marigayin bisa rasuwar da aka yi.

Mafi yawan wadanda suka yi martani sun yabawa Kabiru Gombe bisa wannan ta'aziyya duba da cewa akidarsu ta bambanta da marigayin.

Duk da haka, an samu waɗansu daidaiku da suke nuna rashin jin dadi kan ta'aziyyar da malamin ya yi duba da yadda wasu malamai suke nuna hakan bai dace ba.

Gwamnonin Arewa sun jajanta rasuwar Dahiru Bauchi

An ji cewa kungiyar gwamnonin Arewa ta NSGF ta bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga Musulmai.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce Shehun malamin ya shafe ƙarni yana yaɗa ilimin addini da raya Darikar Tijjaniyya.

Gwamnonin Arewa su 19 sun yi addu’ar Allah ya jikan fitaccen malamin kuma ya saka masa da Aljannatul Firdaus.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.