Sarkin Musulmi Ya Yi Nasiha Mai Ratsa Zuciya kan Rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Sarkin Musulmin ya bayyana rasuwar sanannen malamin addinin a matsayin abin da ke nuna cewa duniya ba wurin zama ba ce
- Sultan III ya mika sako ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, mabiyansa da kuma al'ummar Musulmi gaba daya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta yi ta’aziyya kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamban 2025 yana da shekaru kimanin 101 a duniya.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi a kan rasuwar Dahiru Bauchi?
Kungiyar ta bayyana marigayin a matsayin haske ga al’umma, jagora, da kuma mutum mai jajircewa ga aikin addinin Musulunci, wanda rashin sa ya bar babban gibi da zai yi wuya a cike.
JNI ta ce Sarkin Musulmi ya karɓi labarin rasuwar babban malamin cikin kaduwa da mika wuya ga hukuncin Allah Madaukakin Sarki.
“Mai Alfarma Sarkin Musulmi yana mika ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Dahiru Usman, almajiransa, gwamnatin jihar Bauchi, shugabannin darikar Tijjaniyya da daukacin al’ummar Musulmi bisa rasuwar wannan babban malamin Musulunci."
“Dukkan rayuwarsa ta kasance sadaukarwa wajen hidima ga Al-Kur’ani da karatunsa. Ya tsaya tsayin daka kan akidar da yake bi, tare da kasancewa tushen koyi ga al’umma."
"Ya tabbatar da dorewar aikinsa ta hanyar tarbiyyar da ya ba daruruwan matasa malamai da masu wa’azi, da kuma ’ya’yansa da dama da suka haddace Al-Kur’ani."
“Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta sake tunatar da mu cewa wannan duniya mai wucewa ce; ko da mun daɗe, dole mu amsa kiran Ubangiji.”
- Farfesa Khalid Aliyu Abubakar
An yi nasiha ga Musulmai
Kungiyar ta yi kira ga al’umma da su riƙa tsoron Allah, su yawaita tuba da aikata kyawawan ayyuka, tare da zama masu alheri ga jama’a kafin mutuwa ta riske su, rahoto ya zo a The Nation.

Source: Facebook
Ta kuma bayyana cewa rasuwar marigayin ta kawo karshen wani muhimmin zamani a tarihin ilimin Musulunci a Najeriya.
“JNI na cikin juyayi kan rashinsa, tare da duk wani Musulmi da ya rasu wanda ya bar tarihi mai kyau a kasar nan.”
“Allah Mai Rahma Ya gafarta wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi da sauran ’yan’uwanmu Musulmi da suka riga mu, Ya sanya kaburburansu su zama wuraren hutawa, Ya ba su rahama mai yawa, Ya kuma shigar da su cikin Aljannatul Firdaus. Amin."
- Farfesa Khalid Aliyu Abubakar
Zakzaky ya kadu kan rasuwar Dahiru Bauchi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya yi kadu kan rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Shugaban na kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayin da kuma mabiyansa.
Sheikh Zazkzaky ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga al'ummar Musulmi a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


