Sheikh Zakzaky Ya Fadi Abin da Ya Ji kan Rasuwar Shehu Dahiru Bauchi
- Manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da alhinin rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Jagoran kungiyar Islamic Movement of Nigeria, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya bi sahun masu mika sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar malamin na darikar Tijjaniyya
- Sheikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana rasuwar Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga al'ummar Musulmi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jagoran kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya yi alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Sheikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana bakin cikinsa matuka kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya yi bankwana da duniya a ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban shekarar 2025.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin sakon ta’aziyya da ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky ya fitar a ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi jimamin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Al’ummar Musulmi a Najeriya da ma kasashen waje sun shiga jimami bayan labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usaman Bauchi da aka sanar da sanyin safiyar Alhamis, 27 ga Nuwamba, 2025.
Marigayin ya rasu ne bayan an kai shi asibitin sojoji da ke Bauchi da daddare, inda aka sanar da rasuwarsa bayan Sallar Asuba.
Iyalansa su fitar da sanarwar kan lokacin da za a yi masa Sallah, inda suka bayyana cewa za a yi jana'izar malamin a ranar Jumma'a, 28 ga watan Nuwamban 2025.
Me Zakzaky ya ce kan rasuwar Dahiru Bauchi?
Sheikh Zakzaky ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi mai nauyi ga al’ummar Musulmi gaba ɗaya.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, almajiransa da dimbin mabiyansa kan babban rashin da aka yi
Hakazalika, Sheikh Zakzaky ya roki Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya yi masa rahama, kuma ya ba shi matsayi mai girma a gidan Aljannah.
Sheikh Zakzaky ya kuma yi addu’a Allah Ya ba iyalan mamacin, ’yan uwa da dubban masoyansa haƙuri da ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.

Source: Twitter
Karanta wasu labaran kan rasuwar Dahiru Bauchi
- Gwamna Bala ya yi magana kan rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a asibiti
- Shugaba a Izala, Jalo Jalingo ya yi magana kan rasuwar Shehu Dahiru Bauchi
- Gwamnan Katsina ya fitar da sanarwa bayan saka lokacin jana'izar Dahiru Bauchi
- Nasihar da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi kan mutuwa kafin Allah ya karbi rayuwarsa
- Wasiyya: An saki hotunan wurin da za a birne gawar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Tinubu ya yi alhinin rasuwar Dahiru Bauchi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kadu bayan samun labarin rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Dahiru Bauchi wanda ya bayyana a matsayin mutum mai son zaman lafiya.
Mai girma Tinubu ya kuma bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga iyalansa, mabiyansa da kasa baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

