'Yan Bindiga Sun Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, Sun Yi Garkuwa da Mutane

'Yan Bindiga Sun Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, Sun Yi Garkuwa da Mutane

  • Sabon harin ‘yan bindiga ya jefa al’ummar Gidan-Bijimi, Abuja cikin firgici, inda aka yi garkuwa da mata shida da namiji ɗaya
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar dauke da AK-47 sun shiga gidaje biyu, suka bude wuta kan mai uwa da wabi
  • Wannan hari ya faru ne duk da umarnin Ministan Abuja na ƙara tsaro, wanda ya hada da jibge karin soji, DSS da ‘yan sanda

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fargaba ta sake dawo a yankin Kawu da ke karamar hukumar Bwari ta Abuja, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai sabon hari a daren Laraba.

An rahoto cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da mata shida da kuma wani saurayi dan shekara 16 a wannan hari da suka kai Kwu.

Kara karanta wannan

Ana jimamin sace dalibai, 'yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Neja

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 7 a sabon harin da suka kai Abuja
Babbar kofar shiga babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @OfficialFCTA
Source: Twitter

Wannan na zuwa ne kasa da kwanaki uku bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya umarci jami’an tsaro su ƙara tsaurara tsaro a iyakokin birnin tarayya, in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace mutane a Abuja

Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin sun shiga rudani bayan 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, kuma suka ci karfin 'yan bangar da suka yi yunkurin kawo dauki.

Wani mazaunin garin Kawu, Suleiman Shuaibu, ya tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:47 na daren ranar Laraba.

Suleiman ya ce ‘yan bindigan dauke da AK-47 sun shiga Gidan-Bijimi, suka kutsa cikin gidaje biyu suka kuma yi harbe-harbe ba kakkautawa.

A cewarsa, mata shida da saurayi dan shekara 16 ne aka tafi da su kuma dukkan matan suna tsakanin shekaru 17 zuwa 23, inda ya ce ɗaya daga cikin su ‘yar ƙanwarsa ce.

Kara karanta wannan

Bayan ceto dalibai 25, shaidanin ɗan bindiga ya shiga hannun jami'an tsaro

Ya ce:

“Misalin ƙarfe 9:53 na dare ne aka kira mu cewa ‘yan bindiga sun shiga Gidan-Bijimi. Sun tafi da mata shida, har ma da ɗan uwar ƙawata. Mutane sun rika gudu domin tsira da rai.”

’Yan banga sun yi kokarin dakile 'yan bindiga

Suleiman ya ce wasu ‘yan banga sun yi ƙoƙarin dakile harin, amma sai suka ja da baya saboda ƙarfin makaman ‘yan bindigan ya fi nasu, in ji rahoton Vanguard.

Har yanzu masu garkuwar ba su kira iyalan wadanda suka sace ba, kuma a cewar Suleiman, mazauna garin sun fara yin gudun hijira saboda tsoron hare-hare.

Yanzu haka dai ana jiran jin ta bakin mai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, game da lamarin.

'Yan bindiga sun kai hari Abuja ne jim kadan bayan Wike ya ba da umarnin karfafa tsaro.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya na jawabi a wani taro. Hoto: @OfficialFCTA
Source: Facebook

Wike ya bada umarnin karfafa tsaro a iyakokin Abuja

Harin ya faru ne kwanaki biyu bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ba jami'an tsaro umarnin karfafa tsaro musamman a iyakar Abuja da jihohin Kaduna, Niger da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: 'Yan bindiga sun shiga jihar Kano, sun yi garkuwa da mata

Bayan wannan umarni, an tura rundunar haɗin guiwa ta sojoji, DSS, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa mahimman yankuna domin kawo ƙarshen sace-sace da hare-hare.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Miller Dantawaye, ya ce jami’an tsaro sun samu kayan aiki da isassun motocin sintiri domin gudanar da aikin tsabtace yankunan da ke da barazana.

'Yan bindiga sun kashe likita a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun hallaka wani likitan dabbobi da ke zaune a Abuja, Dr. Ifeanyi Ogbu, a gidansa.

'Yan bindiga sun kashe likitan ne wanda kuma shi ne tsohon shugaban kungiyar NVMA reshen birnin tarayya Abuja, a harin da suka kai.

Bayan sun kashe Dr. Ifeanyi Ogbu, an ce ‘yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kuma sace ‘ya’yansa guda uku.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com