Sheikh Sharif Saleh Zai Yi wa Marigayi Dahiru Usman Bauchi Sallar Jana'iza
- An sanar da cewa Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini ne zai yi wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi sallar jana’iza bisa wasiyyar marigayin
- Iyalan Sheikh Dahiru sun tabbatar da cewa za a yi jana’izar a gidansa da ke Bauchi ranar Juma’a 28 ga watan Nuwamba, 2025
- A wannan rahoton, mun kawo muku wasu muhimman abubuwa game da tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh, babban malami dan darikar Tijjaniyya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Bayan rasuwar babban malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, an fadi wanda zai masa jana'iza.
Wannan sanarwar ta fito ne daga babban ɗan marigayin, Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan wasiyyar da marigayin ya bari.

Source: Facebook
Sayyid Ibrahim ya tabbatar a Facebook cewa fitaccen malamin addini, Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini daga Maiduguri, shi ne zai jagoranci sallar jana’izar Dahiru Bauchi.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci
Al’ummar Musulmi a sassa daban-daban na ƙasar nan suna cigaba da miƙa ta’aziyarsu ga iyalan malamin da kuma mabiyan darikar Tijjaniyya bisa wannan babban rashi da aka yi.
Sharif Saleh zai yi wa Dahiru Bauchi jana'iza
Ibrahim Dahiru Bauchi ya roƙi Musulmi da su cigaba da yin addu’a, yana mai cewa wasiyyar mahaifinsu ita ce Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini ya jagoranci sallar gawarsa.
Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhusaini ɗaya ne daga cikin manyan malamai a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin fitattun malaman darikar Tijjaniyya a ƙasar.
Shi ne shugaban kwamitin Fatwa na Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, kuma ya shahara wajen bayar da fatawoyi da jagoranci a fannonin addini.
Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa an haifi malamin a ranar 12, Mayu, 1938 a garin Aredibe, kusa da karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.
Shi kan shi wannan babban malamin addinin musulunci ya kai shekaru 87 a duniya.
Ya taso cikin gidan malamai, inda mahaifinsa Sheikh Muhammad Al-Saleh bin Yunus Al-Nawwy ya yi fice wajen koyar da ilimin addini da tarbiyya.

Source: Facebook
Sheikh Sharif ya yi karatu a Najeriya da ƙasashen waje, inda ya kware a harshen Larabci, Turanci, Hausa da Kanuri.
A bangaren ilmin addini, malamin ya yi fice musamman a wajen hadisan Manzon Allah SAW, fikihu da kuma Tafsirin Kur'ani mai tsarki.
Yana cikin malaman da suka yi tasiri ga dubban mabiyan Tijjaniyya, musamman wajen bayar da ilimi, jagoranci da koyar da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Wurin da lokacin jana’izar Dahiru Bauchi
A wata sanarwa da iyalan marigayin suka fitar, an tabbatar da cewa za a masa jana’iza ne a yau, 28, Nuwamba, 2025 bayan sallar Juma'a a garin Bauchi.
Ana sa ran cewa mutane daga jihohi da dama na Najeriya da ma kasashen waje za su halarci jana'izar malamin.
Sanata Barau ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi
A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi ta'aziyyar rasuwar Shehu Dahiru Bauchi.
Sanata Barau ya bayyana cewa rasuwar malamin ta bar gibi babba a Najeriya lura da gudumawar da ya bayar.
Ya kuma roki Allah ya gafarta masa kurakuransa tare da yi wa jihar Bauchi da iyalan malamin jajen babban rashin da suka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

