Hardar Kur'ani: Sheikh Dahiru Bauchi da Zuriyarsa Sun Kafa Tarihi a Duniyar Musulunci

Hardar Kur'ani: Sheikh Dahiru Bauchi da Zuriyarsa Sun Kafa Tarihi a Duniyar Musulunci

  • Shehin malamin Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi ya zama mutum na farko a duniya da ya tara zuriyar da ta fi ko wacce yawan mahaddatan Alƙur’ani
  • Rahoto ya nuna cewa Allah Ya albarkaci Dahiru Bauchi da ’ya’ya, jikoki da tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alƙur’ani mai girma
  • Kundin Cholan Book of World Records ya tabbatar da wannan tarihi na malamin, wanda ya rasu ranar 27 Nuwamba, 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Ana ci gaba da jimami da alhinin rasuwar babban malamin darikar Tijjaniya a Najeriya da nahiyar Afirka, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Alkaluma sun nuna cewa marigayin, wanda kwanan nan ya haura shekara 100, yana da ’ya’ya, jikoki da tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alƙur’ani mai girma.

Sheikh Dahiru Bauchi.
Sheikh Dahiru Bauchi tare da data daga cikin 'ya'yansa Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Tarihin da Sheikh Dahiru Bauchi ya kafa

Kara karanta wannan

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta girgiza Sanata Barau, ya fadi yadda ya ji

Kundin Cholan Book of World Records ya bayyana shi a matsayin mutum na farko a tarihin duniya da ya samu wannan baiwar ta zama uba ga zuriya mafi yawan mahaddatan Alƙur’ani, in ji rahoton Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya nuna cewa Sheikh Dahiru yana da ’ya’ya 95, jikoki 406, tattaba-kunne 100 kuma daga cikin wannan adadi, ’ya’ya 77, jikoki 199 da tattaba-kunne 12 ne suka haddace Alƙur’ani.

Shehin malamin ya rasu a safiyar Alhamis, 27 Nuwamba 2025, a garin Bauchi bayan an garzaya da shi asibiti.

Tuni dai malamai da sauran al'ummar Musulmi suka fara tura sakon ta'aziyya tare da addu'ar Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kura-kuransa.

Iyalan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi sun sanar da cewa za a yi masa jana'iza tare da kai shi makwancinsa a ranar Juma'a, 28 ga watan Nuwamba, 2025 a jihar Bauchi.

Khalifan Sheikh Inyass a Najeriya

Sheikh Dahiru Usman Bauchi yana daga cikin khalifofin Shehu Ibrahim Inyass, jagoran Darikar Tijjaniyya bayan wanda ya assasa ta na farko, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.

Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, kuma shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli ta Fatawar Musulunci a Najeriya kuma Fitaccen jigo a Darikar Tijjaniyya ta kasar nan da ma wasu sassan Afirka.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya fitar da sanarwa bayan saka lokacin jana'izar Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi.
Hoton babban Shehun Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi
Source: Facebook

A wata tattaunawa da aka yi da shi a Bauchi wasu shekaru da suka gabata, Sheikh Dahiru ya bayyana asalinsa da cewa:

Ya ce:

"Tarihina dai ni Bafulatani ne. Dukan kakannina hudu Fulani ne, na wajen mahaifi biyu, na wajen mahaifiya biyu. Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata kuma Bafulatanin Nafada ne a Jihar Gombe.”

Nasihar Sheikh Dahiru Bauchi kan mutuwa

A baya, mun kawo muku nasihar da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wa al'ummar musulmi kan duniya da kuma mutuwa wacce ke kan wuyan kowa.

A 'daya daga cikin karatuttukan da ya yi a lokacin rayuwarsa, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce rayuwar duniya ba komai ba ce ga dan Adam.

Ya shawarci mutane su lazimci tunanin mutuwa da tuna radadin da ake sha wajen mutuwa, yana mai shawartar mutane da su roki Allah Ya yaye masu zafin fitar rai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262