Nasihar da Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yi kan Mutuwa kafin Allah Ya Karbi Rayuwarsa
- Ana ci gaba da alhini da jimamin rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Rasuwar Shehun Tijjaniyyan ta ja hankalin Musulmi musamman a Arewacin Najeriya, inda ake ta masa addu'a da fatan samun rahama
- A lokacin da yake raye, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wa jama'a nasiha kan mutuwa da radadin da ake sha a lokacin fitar rai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Da safiyar yau Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 aka wayi gari da labarin rasuwar fitaccen malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa malamin ya rasu ne a wani asibiti da aka kwantar da shi bayan jikinsa ya motsa a jihar Bauchi, ya rasu yana fa shekaru 100 a duniya.

Source: Facebook
Iyalai sun tabbatar da rasuwar malamin
Daya daga cikin 'ya'yansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ya tabbatar da rasuwar mahaifinsu ga jaridar Daily Trust ta wayar salula yau Alhamis da safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jima kadan bayan bullar wannan labari, mutane suka fara nuna alhini da jimamin rashin fitaccen malamin, wanda ke da miliyoyin mabiya a ciki da wajen Najeriya.
A wani faifan bidiyo da shafin Darika TV ya wallafa a Facebook, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wa al'ummar Musulmi nasiha kan rayuwar duniya da mutuwa a lokacin da yake raye.
A 'daya daga cikin karatuttukan da ya yi a lokacin rayuwarsa, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce rayuwar duniya ba komai ba ce ga dan Adam.
Nasihar Sheikh Dahiru Bauchi kan mutuwa
A cewarsa, duniya ba wurin kwanciya ba ce ga mutane, inda ya ba da misali da cewa tamkar mutum ne ya fito za shi wani wuri, sai ya biyo ta duniya kafin ya tattara kayansa ya tafi inda ya nufa.
Ya shawarci mutane su lazimci tunanin mutuwa da tuna radadin da ake sha wajen mutuwa, yana mai shawartar mutane da su roki Allah Ya yaye masu zafin fitar rai.
A nasihar da ya yi, Shehin Malamin ya ce:
"Duniya ba wurin kwanciya ba ne, ka fito wani wuri ne, za ka wani wuri sai ka biyo ta duniya, saboda haka kar ka yi sake, ka lazimci tunanin mutuwa da bakin cikin da ake samu wurin mutuwa."
"Ka roki Allah Ya yaye maka, ya zama mutuwar ta zo maka da sauki. Sannan ka yi tunanin tambayar da ake yi a kabari, Allah Ya ba mu da sauki albarkacin Shehu Tijjani."

Source: Facebook
Gwamna Bala ya mika sakon ta'aziyya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana alhini bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Ya ce darussan da ya gudanar a wurare daban-daban da tsangayoyinsa sun tara ɗaruruwan almajirai waɗanda suka haddace Qur’ani tare da yada ilimin Musulunci a Nahiyar Afirka baki ɗaya.
A madadin iyalinsa, gwamnatin Bauchi da al’ummar jihar, Gwamna Bala ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, almajiransa, mabiyansa da daukacin al’ummar Musulmi a Najeriya da ma kasashen waje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

