'Ba Alhamis ba ne,' An Sanya Lokacin da Za a Yi Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi
- An shiga cikin tsananin jimami a Bauchi, Najeriya, Afrika da duniya baki daya bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
- Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kasance fitaccen malamin Musulunci kuma jagoran darikar Tijjaniyya na Afrika
- Iyalan marigayin sun sanar da cewa za a gudanar da jana'izar malamin a garin Bauchi, amma ba a yau Alhamis ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - An sanya lokacin da za a gudanar da jana'izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Legit Hausa ta ruwaito cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu ne da sanyin safiyar Alhamis, 27 ga Nuwambar 2027 a jihar Bauchi.

Source: Facebook
An sanya lokacin jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi
Wata sanarwa da jaridar Aminiya ta fitar a shafinta na Facebook ta nuna cewa za a gudanar da jana'izar malamin ne a gobe Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya bayyana cewa:
"Iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun sanar da cewar za a yi jana’izar marigayin, a gidansa da ke Bauchi a ranar Juma'a."
Hakazalika, sanarwar kungiyar Fityatul Islam da aka wallafa a shafinta na Facebook ya nuna cewa:
"Za'a gudanar da sallah jana'iza na Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi gobe Juma'a, 28 ga Nuwamba, 2025, a garin Bauchi."
Mutane sun taru a masallacin Dahiru Bauchi
Jim kadan bayan sanar da rasuwar malamin, an ce gomman mutane sun fara tururuwa a masallacinsa da ke cikin kwaryar Bauchi.
Wani ma'abocin Facebook, Umar Haruna Danmajalisa, ya wallafa a shafinsa cewa mutane sun fara taruwa a masallacin, da tunanin za a iso da gawar malamin.
Hade da wasu hotuna, Umar Danmajalisa ya wallafa cewa:
"Allahu Akbar!
"Hakika wannan rana ce mai cike da jimami da tunani. Jama’a sun fara taruwa a harabar masallacin Shehu Dahiru Usman Bauchi domin jiran isowar gawar wannan babban malami, jagora, shugaba, kuma fitilar addini.
"Allah Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa kabarinsa ya kasance lambun aljanna.
"Allah Ya ba al’ummar Musulmi hakurin jure wannan babban rashi, Ya maye mana gurbin sa da mafi alheri.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un."
Kalli hotunan a kasa:
Jama'a sun yi jimamin rasuwar Dahiru Bauchi

Source: Facebook
'Yan Najeriya sun mamaye shafukan sada zumunta suna ta'aziyyar Sheikh Dahiru Bauchi, jagoran darikar Qadiriyya.
Mohammed Umar:
"Allahu Akbar. Allah ya gafarta masa zunubansa, ya sa Aljannah makomarsa."
Mohammed Suleiman:
"Allah ya jikansa da rahama."
Noa Charanci Lga
"Hakika abin da Allah ya dauka nasa ne, kuma abin da ya bayar shi ma nasa ne, kuma ko wanne abu a wurinsa ya na da ajali abin ambato. Sai mu yi hakuri, mu nemi lada (na hakurin rashin da a kayi).
"Allah ya girmama ladar mu, ya kyautata hakurin mu akan wannan babban rashi da muka yi, ya gafartawa magabatan mu, ya albarkaci bayan su."
Alkasim Bin Mai Yaki:
"Allah ka gafarta wa maulana sheikh da rahama bijahi Sayyidil khalki."
Zakiru Dangatan Sayyidah Fadima:
"Tabbas aikin ne ya kammala, ya amsa kiran Allah (SWT) ya je ya huta, sauka lafiya maulana shehi.
"Allah ya kara kusantashi da babban masoyinshi masoyinmu Annabi Muhammadu (SAW). Allahu Akbar lokacin haɗuwar masoyi da masoyi yayi."
Gwamna ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana alhini bisa rasuwar malamin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi.
Babban malamin Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne a ranar 27 ga Nuwamba, 2025 a wani asibiti a cikin garin Bauchi.
Gwamna Bala ya bayyana marigayin a matsayin babban malami a fagen ilimin Musulunci, wanda ya shahara da kamala, tawali’u, tsantseni da hikima.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


