Kamar Kano, Gwamna Radda Ya Kafa Tarihi a Kasafin Kudin Jihar Katsina na 2026
- Gwamna Dikko Radda ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2026 bayan Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da shi
- Kasafin, wanda zai lakume ₦897.8bn ya kunshi 81% na ayyukan ci gaba, da kuma 18% na harkokin gudanarwar gwamnati
- Gwamnatin Katsina ta tsara kashe wadannan kudi a kasafin ne bayan sauraron shawarwarin jama’a a dukkan gundumomi 361 na jihar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - A karo na farko a tarihi, jihar Katsina za ta kashe sama da Naira biliyan 800 a kasafin kudin shekarar 2026.
Gwamna Dikko Umar Radda, a ranar Laraba ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026, kwanaki 22 kacal bayan gabatar da shi ga Majalisar Dokoki ranar 4 ga Nuwamba.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dikko Radda ya kafa tarihi a Katsina
Kasafin mai taken “Building Your Future III” watau gina goben al'umma zai lakume kudi har ₦897,865,078,252.05, kuma shi ne irinsa na farko a tarihin Katsina.
Bugu da kari, kasafin kudin ya ba da fifikon ci gaban jama’a da raya kasa ta hanyar ware kashi 81 ga ayyukan ci gaba da kashi 18 ga ayyukan gudanarwar gwamnati.
Da yake rattaba hannu a fadar gwamnati, Gwamna Radda ya yabawa Majalisar dokokin Katsina bisa yadda ta yi gaggawa wajen zartar da kasafin kudin.
A cewarsa, hakan alamar sadaukarwa, haɗin kai da zumunci ne tsakanin bangarorin gwamnati.
“Gaggawar da majalisa ta yi ta nuna sadaukarwa da kishin ƙasa. A Katsina, bangarorin gwamnati, zartaswa, majalisa da shari’a, suna aiki cikin hadin kai da daidaito domin ci gaban jihar."
“Wannan kasafin na jama’a ne. Mun tattara ra’ayoyi daga mazabu 361 ta hanyar tarukan jin ra'ayin jama'a domin kasafin ya fito daga bukatun mutane.”

Kara karanta wannan
Rigiji gabji: Gwamnan Legas ya gabatar da kasafin kudin Naira tiriliyan 4 na 2026
- Dikko Radda.
Abin da ya sa Majalisa ta amince
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Katsina, Rt Hon. Nasiru Daura, ya ce mambobin majalisa sun yi nazari sosai a kan kasafin da aka gabatar.
Ya ce Majalisar ta kuma binciki dukkan bayanan da ya dace domin tabbatar da cewa kasafin kudin ya dace da bukatun jama’a.

Source: Facebook
Hon. Nasiru Daura ya ce bayan wannan nazari:
"Mun tabbatar kasafin ya yi daidai da tsarin cigaban wannan gwamnati, saboda haka ba mu canja komai ba a jimillar kuɗin.”
Gwamnan Legas ya gabatar da kasafin 2026
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya gabatar da.kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda zai ci sama da Naira tiriliyan hudu ga majalisar dokoki.
A jawabin da ya gabatar wa ’yan majalisa, Sanwo-Olu ya bayyana cewa kasafin ya kunshi tsare-tsare da za su inganta rayuwa jama'a, bunkasa tattalin arziki da sauransu.
Ya ce an ware fiye da N2.18tn domin manyan ayyukan raya kasa, yayin da aka ware N2.05tn domin kudin gudanarwa, wanda ya shafi kudin ma’aikata, biyan bashi da sauran ayyukan gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng