Shehin Darikar Tijjaniyya, Dahiru Usman Bauchi Ya Rasu

Shehin Darikar Tijjaniyya, Dahiru Usman Bauchi Ya Rasu

  • An tabbatar da rasuwar fitaccen malamin addini Sheikh Dahiru Usman Bauchi a daren da ya gabata daga majiya mai tushe
  • Rahotanni sun bayyana cewa za a sanar da rana da lokacin jana’izar jagoran darikar Tijjaniyya nan gaba kadan
  • Addu’o’i da ta’aziyya sun mamaye kafafen sada zumunta tun bayan bazuwar labarin rasuwar malamin da safiyar yau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – Fitaccen malamin addinin Islama kuma jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya da Afrika, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewa ya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ne a cikin daren da ya gabata.

Dahiru Usman Bauchi da ya rasu
Shehu Dahiru Usman Bauchi kafin rasuwarsa. Hoto: Naziru Usman
Source: Facebook

Bayan bazuwar rasuwar malamin a kafafen sada zumunta, RFI Hausa ta ce wata majiya mai tushe ta tabbatar mata da cikawarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce iyalan gida da manyan mabiya za su sanar da cikakken jadawalin jana’izarsa a cikin ‘yan awanni masu zuwa.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fadi yadda ya rungumi Sufanci

Martani bayan labarin rasuwar Dahiru Bauchi

Tuni al’umma daga sassa daban-daban na duniya suka fara aikawa da sakonnin ta’aziyya da addu’a ta kafafen sada zumunta.

Daruruwan mutane ke yabon irin gagarumar rawar da Shehun ya taka wajen yada ilimi, zaman lafiya da hadin kan al’umma.

Wasu na cewa irin gudummuwar da Sheikh Dahiru ya bayar, musamman wajen karantar da Alkur’ani da tarbiyyar matasa, na daga cikin abubuwan da za su dade ana tunawa da shi.

A halin yanzu, mabiyansa da masoya suna ci gaba da addu’ar Allah Ya gafarta masa yayin da ake jiran bayani game da lokacin jana'iza.

Legit ta tattauna da Ibrahim Aminu Ilela

A tattaunawa da wani mazaunin jihar Bauchi, Ibrahim Aminu Ilela, ya yi wa Legit Hausa karin haske game da halin da ake ciki a gidan Shehin.

Ibrahim Aminu Ilela ya ce:

"Ka san dama gidansa a unguwar mu ta Ilela ya ke. Jiya cikin dare aka dauke shi zuwa asibitin sojoji da ke hanyar Ningi amma daga zuwa ba a gane lamarin sosai ba.

Kara karanta wannan

Kiristocin jihohin Arewa 19 sun yi magana kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

"Ana tunanin ma tun a lokacin ya rasu, amma ba a sanar ba.

Ibrahim Ilela ya kara da cewa:

"Sai bayan kammala sallar Asuba, mutane sun fara watsewa aka sanar da rasuwar."

Halin da ake ciki a gidan Dahiru Bauchi

Ibrahim Ilela ya ce a yanzu haka gidan Dahiru Bauchi a rufe ya ke, ba a barin mutane su shiga kai tsaye.

Ya ce:

"Mutane ba su shiga can cikin gidan a halin yanzu. Sai dai masallacinsa ko harabar gidan.
"Idan ka ga mutum ya shiga to sai dai babban dalibinsa ko wani babban mutum."

Ibrahim Ilela ya ce yanzu haka mutane sun taru sosai a unguwar ana ta jimami gane da rasuwar malamin.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Hoto: Ibrahim Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Dr Jalo ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

A wani rahoto, mun kawo muku cewa shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi ta'aziyyar rasuwar Shehu Dahiru Bauchi.

Legit Hausa ta gano cewa Ibrahim Jalo Jalingo ya roki Allah ya gafarta wa marigayin kurakuran da ya yi a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Yadda jikin Shehu Dahiru Bauchi ya yi tsanani, aka tafi da shi asibiti ya rasu

Mutane da dama sun yi magana a karkashin rubutun da Dr Jalo ya yi, inda mafi yawa suka yi addu'o'i ga marigayin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng