Tinubu Ya Nada Shugaban NIA da Ya Shiga Badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen mutane uku ga majalisar dattawa domin tantance su a matsayin jakadu
- Daya daga cikin mutanen da aka nada an taba gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin halatta kudin haram lokacin da yake ofis
- Ayo Oke wanda ya shugabanci hukumar leken asiri ta kasa (NIA), ya rasa kujerarsa a lokacin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ayo Oke a matsayin jakada.
Mai girma Bola Tinubu ya nada Ayo Oke ne tare da wasu mutane biyu domin wakiltar Najeriya a kasashen waje.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Tinubu ya aika da sunayen mutanen ne a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An taba kai jakadan Tinubu kotu
Jaridar The Cable ta ce a baya hukumar EFCC ta taba shigar da kara kan Ayo Oke kan zargin halatta kudaden haram.
Daga baya hukumar EFCC ta janye karar da ta shigar kan tsohon shugaban na NIA, dangane da gano dala miliyan $43m, £27,000 da kuma Naira miliyan 23 a wani ɗaki da ke Ikoyi.
A ranar Juma’a, 9 ga watan Yunin 2023, mai shari'a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas, ya kori shari’ar gaba ɗaya.
Dakatar da shari’ar ta fito ne daga bangaren EFCC, kuma ba a samu wani kalubale daga lauyan Ayo Oke, Kayode Ajulo na Castle of Law Chambers, ba.
An dakatar da shari’ar ne bisa dalilai na tsaron ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da dakatar da shari’ar kafin ya bar mulki.
Wane zargi aka yi wa Ayo Oke?
A watan Afrilu 2017, EFCC ta ce ta gano $43m, £27,000 da N23m a cikin wani gida da ke Osborne Road a Ikoyi, bayan samun bayanan sirri daga wani mai tona asiri.
Bayan nan kuma rahotanni suka bayyana cewa kudaden mallakin hukumar NIA ne.
Hukumar NIA dai ta karɓi $289,202,382 a matsayin kuɗin aiki na musamman daga asusun NAPIMS da ke Babban Bankin Najeriya (CBN) a watan Fabrairu 2015.
NIA ta ce kuɗin suna cikin “aikin leken asiri na ɓoye”, amma jama’a da dama sun yi zargin sace su aka yi.

Source: Twitter
Kwamitin mutane uku karkashin mataimakin shugaban ƙasa na wancan lokaci, Yemi Osinbajo, ya same Ayo Oke da laifi tare da ba da shawarar sallamarsa, wanda aka aiwatar a watan Oktoban 2017.
A ranar 20 ga Janairu 2019, Osinbajo ya ce za a gurfanar da Ayo Oke da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, bisa zarge-zargen aikata laifuffuka, bayan umarnin da Buhari ya bayar.
ADC ta soki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta ragsrgaji gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro.
ADC ta yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na amfani da dabarar da ke karfafa tattalin arzikin 'yan bindiga.
Hakazalika ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta gayawa 'yan Najeriya gaskiya kan halin da ake ciki kan rashin tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


