'Yan Majalisa Sun Fara Shiga Matsala bayan Tinubu Ya Janye 'Yan Sandan da ke Gadinsu

'Yan Majalisa Sun Fara Shiga Matsala bayan Tinubu Ya Janye 'Yan Sandan da ke Gadinsu

  • Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon Idris Wase, ya ce ’yan bindiga na yi wa ’yan Majalisa barazanar garkuwa da su
  • 'Dan Majalisar ya roki Shugaba Bola Tinubu ya sake duba umarnin da ya bayar na janye ’yan sandan masu gadin manyan kasa (VIP)
  • Gwamnatin Tarayya ta ce manufar janye jami’an ita ce ƙara yawan ’yan sanda a yankunan da ba su da isasshen tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa ’yan bindiga sun fara barazanar sace wasu daga cikin ’yan Majalisa.

Hon. Ahmed Wase ya bayyana haka ne yayin da ake muhawara kan tabarbarewar tsaro a Majalisar Wakilan Tarayya ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2025.

Hon. Idris Wase.
Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Idris Wase Hoto: @HonAhmedIdrisWase
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta tattaro cewa Majalisar Wakilai ta tattauna da nufin lalubo mafita kan karuwar hare-haren 'yan bindiga a wasu sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: ADC ta jefa zafafan tambayoyi ga gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Idris Wase ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake duba umarnin da ya bayar na janye ’yan sandan da ke gadin manyan mutane (VIPs).

Umarnin Tinubu na janye ’yan sanda

A ranar Lahadi, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin janye gaba daya 'yan sandan da ke gadin kanyan mutane, wanda ya kunshi 'yan Majalisa da sauran shugabanni.

Bola Tinubu ya bada wannan umarnin a wani taron tsaro da aka yi a Abuja tare da hafsoshin tsaro da shugaban hukumar DSS.

Mai girma shugaban kasa ya bayyana cewa ya dauki matakin janye ’yan sandan ne domin mayar da su kan aikin su na asali watau tsaron al’umma a fadin ƙasar nan.

Dalilin Tinubu na janye 'yan sanda

Da wannan sabon tsarin, rundunar 'yan sanda ta umurci sashe na musamman Special Protection Unit (SPU) ta kira duk jami’anta daga wurin manyan da suka gadi su koma sansanoninsu.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi matsayin da 'yan bindiga suka samu a gwamnatin Tinubu

Shugaba Tinubu ya ce duk wani babban mutum a kasa da ke buƙatar kariya a yanzu ya nemi jami’an tsaro daga hukuma NSCDC, ba daga rundunar ’yan sanda ba.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen ƙara yawan ’yan sanda a cikin al’umma, musamman yankunan karkara da babu isassun jami’ai, inda mazauna ke fuskantar hare-hare.

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Hon. Wase ya roki Bola Tinubu

Sai dai Hon. Idris Wase ya bukaci Shugaba Tinubu ya sake duba wannan umarni, kuma ya kara yin bayani kan mutanen da matakin ya shafa, cewar The Cable.

Ya tuna wani lokaci da aka gano cewa ’yan Boko Haram sun kutsa cikin jerin waɗanda aka dauka aiki a Rundunar Sojoji da ta ’Yan Sanda.

“Akwai wani lokaci da aka gano ’yan Boko Haram a cikin jerin wadanda aka dauka aiki. Saboda haka, dole a fayyace su waye ake kira da VIP.”

Sanatoci sun tabo batun tsaron Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta Najeriya ta yi zazzafar muhawara kan kara tabarbarewar tsaro a ƙasar nan, musamman a jihohin Kwara, Kebbi da Neja.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Neja sun fusata, sun shirya daukar mataki kan jinkirin ceto daliban Papiri

Yayin muhawarar, Mataimakin Shugaban Majalisa, Sanata Barau Jibrin, ya ce za a iya magance matsalar tsaron Najeriya amma sai an nemi taimako daga ketare.

Wasu daga cikin 'yan Majalisar Dattawa sun fara goyon bayan kafa dokar hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262