An Kashe Mutum 2 da Ƴan Bindiga Suka Je Sace Dalibai a Kogi? Gwamnati Ta Yi Martani

An Kashe Mutum 2 da Ƴan Bindiga Suka Je Sace Dalibai a Kogi? Gwamnati Ta Yi Martani

  • 'Yan bindiga sun kashe mutum biyu a harin da suka kai makarantar Kiri da ke karamar hukumar Kabba-Bunu, jihar Kogi
  • Shugaban karamar hukumar, Barista Zacheus Dare, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an dakile wannan hari
  • Gwamnatin Kogi ta karyata jita-jitar an yi garkuwa da ɗaliban makarantar, tare da barazanar kama masu yada karyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - A kalla mutum biyu sun rasa rayukansu lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari makarantar Kiri da ke Aiyetoro Kiri.

Legit Hausa ta fahimci cewa garin Aiyetoro Kiri na cikin karamar hukumar Kabba-Bunu, da ke a jihar Kogi.

Ana fargabar 'yan bindiga sun yi yunkurin sace dalibai a Kogi amma mafarauta da 'yan sa kai suka dakile su.
Taswirar jihar Kogi da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi yunkurin sace dalibai a Kogi

'Yan ta'addar sun kai harin ne a safiyar ranar Laraba, inda mafarauta da ‘yan sa-kai suka dakile harin kafin ‘yan bindigar su samu damar sace ɗalibai, in ji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Neja: Wasu dalibai da aka sace sun yi dabara, sun gudo daga hannun 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban karamar hukumar Kabba Bunu, Barista Zacheus Dare, ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da gidan talabijin din ta wayar salula.

Barista Zacheus Dare ya bayyana cewa ba a sace kowa ba, kuma jami’an tsaro na cikin daji suna bin sawun ‘yan bindigar.

Barrister Dare ya bayyana cewa:

“Mutum biyu ne suka mutu—wani mafarauci da kuma wani mutum da aka harba. Ba a sace ɗalibi ko guda ba. Mun tsaya a garin har zuwa wayewar gari.”

Gwamnati ta karyata rahoton sace dalibai

Shugaban karamar hukumar ya ce sojoji, ‘yan sanda, mafarauta da sauran jami’an tsaro na ci gaba da aikin farautar ‘yan bindigar a daji domin hana su dawowa.

Sai dai jim kadan bayan faruwar lamarin, wata jita-jita ta yadu a Facebook cewa an yi garkuwa da daliban makarantar Kiri.

Wannan ya sa mai ba gwamnan Kogi shawara kan tsaro, Commander Jerry Omodara (mai ritaya), ya fito karara ya karyata labarin, in ji rahoton TVC News.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ce ana shirin aikin da zai dagula kokarin ceto daliban Kebbi

Ya ce labarin ƙarya ne daga mutanen da ke kokarin tada hankalin jama’a da kawo rudani a cikin al’umma.

“Abin mamaki ne yadda wasu mutane ke ƙirƙiro labaran da za su haddasa tashin hankali,” in ji Commander Omodara.
Gwamnatin Kogi ta ce babu wani harin 'yan bindiga a makarantar Riki.
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo ya na jawabi a gidan gwamnati. Hoto: @kogistategovng
Source: Facebook

Gwamnati za ta kama masu yada labaran karya

Omodara ya ce gwamnati ta fara bibiyar mutanen da suka yada labarin domin hukunta su bisa dokokin kasa.

Omodara ya kuma tabbatar wa jama’a cewa dukkan hukumomin tsaro suna cikin shirin ko-ta-kwana a fadin jihar, ana kuma bibiyar duk wani motsi da ka iya barazana ga zaman lafiya.

Ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya tare da bayar da bayanan sirri ga hukumomin tsaro idan sun ga wani motsi da basu yarda da shi ba.

'Yan bindiga sun sace babban soja a Kogi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sace tsohon Manjo, Joe Ajayi mai shekaru 76 a gidansa da ke Odo-Ape, Kabba-Bunu, jihar Kogi.

Maharan sun mamaye yankin, tare da bude wuta ta ko ta ina, kafin su yi awon gaba da tsohon sojan da ke fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

An kama wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kashe Kiristoci a Kwara? Gaskiya ta fito

Garkuwar da aka yi da Manjo Ajayi ta jefa al’umma cikin fargaba, tare da ƙara tabbatar da gargadin da kungiyar ci gaban Okun (ODA) ta yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com