‘Ka Tanadi Hujjoji’: Pantami Zai Iya Shiga Kotu da Aka Zarge Shi da Kisan Dalibin ATBU
- Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya fusata kan wasu zarge-zarge da ake yadawa kansa game da zargin tsattsauran ra'ayi a baya
- Malamin ya karyata zargin kisan kai baki ɗaya, yana cewa ba ya da hannu kai tsaye ko a kaikaice inda ya gargadi masu yada hakan
- Ya nemi bayanan masu zargi domin daukar matakin shari’a, yana mai bayyana dogaro da bayanan AI kamar Grok a matsayin kuskure
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna bacin ransa kan zarge-zarge da suke yawo a kafofin sadarwa game da shi.
Sheikh Isa Pantami ya bayyana hakan ne yayin da wasu ke zargin ya umarci kisan wani dalibi a Jami'ar ATBU a shekarun baya.

Source: Facebook
Malamin addinin ya karyata zarge-zargen da ake alakantawa da shi a yau Laraba 25 ga watan Nuwambar 2025 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pantami ya bukaci a kai shi kotu
Sheikh Pantami ya ce dogaro da fasahar AI irinsu Grok wurin neman bayanai a matsayin kuskure kuma zai iya daukar matakin shari'a.
Tsohon ministan ya bukaci mutumin da ya tanadi hujjoji domin kai shi kotu idan har yana da gaskiya idan kuma ba haka ba zai iya shiga shari'a da shi.
Ya ce:
“Na gode da ka bayyana ra’ayinka. Kana yi mini zargi wanda babu kamshin gaskiya ko kadan ba, Ban taɓa kashe ko umartar kisan kowa ba a rayuwata, ko kai tsaye ko a kaikaice.
"Idan kana da hujja a kan haka, don Allah ka taimaka wa ‘yan uwan mamacin ka kai maganar kotu.
"Ko kuma, idan kana da ƙarfin guiwa, ka ba da cikakkun bayananka domin in kai ka kotu kan wannan zargi na ƙarya."

Source: Facebook
Gargadin da Pantami ya yi wa mutumin
Sheikh Pantami ya ce kwata-kwata samo bayanai daga manhajojin AI akwai kuskure domin ba dole su ba da bayanan gaskiya ba.

Kara karanta wannan
Abin da ya sa Sheikh Gumi ya fi damuwa da 'yan bindiga fiye da wadanda ake kai wa hari
Ya kuma gargadi wanda ya ke zargin na shi da ya ba da bayanansa idan ba tsoro ba domin su hadu a kotu inda ya tabbatar da cewa bai taba umartar kisan wani ba.
"Grok da sauran na’urorin AI da kake dogaro da su suna samun bayanai ne daga yanar gizo, kuma sau da yawa bayanan ba su da inganci. Idan kana da tabbas kan zarginka, ka bi hanyar doka.
"Idan ba haka ba, ka ba ni bayananka na gaskiya domin mu hadu a kotu, domin kara wayar maka da kai, ban taɓa yin wata huduba ko umarni da ya shafi kashe kowa ba."
Pantami ya yi Allah-wadai da hare-hare
Mun ba ku labarin cewa tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi magana kan hare-haren da ake fama da su a Najeriya.
Majidadin na Daular Usmaniyya ya yi Allah-wadai kan yadda hare-haren suka jawo asarar rayuka da sace mutane.
Hakazalika, ya ba hukumomin tsaro shawarar hanyar da ya kamata su bi domin cafke mutanen da ke aikata irin wadannan laifuffuka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
