Gwamnatin Kano Ta Zo da Matsala, An Samu Tsaiko a Shari'ar Ganduje da Wasu Mutum 7
- Babbar Kotun Kano ta dage shari’ar tsohon shugaban APC, Dr Abdullahi Ganduje da wasu mutum bakwai zuwa 3 ga Fabrairu, 2026
- Gwamnatin Kano ta gurfanar da su kan tuhuma 11 da suka shafi cin hanci, cuwa-cuwa da karkatar da biliyoyin Naira a gwamnatin baya
- Alkali kotun ya amince da buƙatar ƙara wa gwamnatin Kano lokacin amsa ƙorafe-ƙorafen da ake yi da su a shari'ar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta kawo tsaiko a zaman shari'ar tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje.
Gwamnatin Kano ta maka Ganduje gaban kotu tare da matarsa Hajiya, Hafsat Umar, da wasu mutane shida bisa tuhuma 11.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa tuhume-tuhumen sun hada da cin hanci, hada baki, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma almundahana da ya kai darajar biliyoyin Naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran waɗanda ake tuhuma tare da tsohon gwamna Ganduje da matarsa su ne, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad.
Saku kuma kamfanonin Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited.
Yadda gwamnatin Kano ta kawo tsaiko
Lokacin da aka dawo zaman shari’ar a yau Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2025 lauyan gwamnatin Kano, Jedidiah Akpata ya shaida wa kotu cewa ba su shirya ci gaba da zaman ba.
Ya ce:
"Mai girma mai shari'a, ba mu shirya ci gaba ba. Muna neman izinin kotu domin mu gabatar da buƙatar neman ƙarin lokaci.”
Akpata ya nemi ƙarin lokaci domin mayar da martani kan korafin neman dakatar da shari’a da waɗanda ake tuhuma suka shigar tun ranar 19 ga Nuwamba, 2025.
Haka kuma ya shigar da wata buƙatar ƙarin lokaci a ranar 24 ga Nuwamba domin amsa ƙorafin wanda ake tuhuma na shida.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Sojojin Najeriya sun kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Taraba
Lauyan Ganduje ya shirya tsaf
Lauyan Ganduje, matarsa da ɗansa, Lydia Oluwakemi-Oyewo, ta ce su sun shirya ci gaba da shari’ar, amma ba su adawa da buƙatar ƙarin lokaci da gwamnati ta nema.
Lauyoyi sauran waɗanda ake tuhuma ciki har da Cif M. N. Duru (SAN), Abdul Adamu-Fagge (SAN), Abubakar Ahmad, da Abdulrazaq A. Ahmed, suma duk sun ce a shirye suke.

Source: Twitter
Kotu ta amince da buƙatar gwamnati
Alkalin kotun, Mai Shari'a Amina Adamu-Aliyu ta amince da buƙatar ƙarin lokaci da gwamnati ta nema sannan ta dage shari’ar zuwa 3 ga Fabrairu, 2026, domin sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen da ake da su.
Rahoton Punch ya nuna cewa wannan shari’a ta rika fuskantar dage-dage da dama a baya saboda irin wannan dalili
Ganduje zai kafa wata hukumar Hisbah
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana shirin kafa wata kungiyar tsaro a jihar domin samar da zaman lafiya.
Ganduje ya ce shirin na nufin daukar ma’aikatan Hisbah 12,000 da gwamnatin yanzu ta kora, yana mai jaddada cewa ba a bi hanyar da ta dace wajen korarsu ba.
Ya ce sabon tsarin zai kasance kamar Hisbah mai zaman kanta ba hukumar gwamnati ba, kuma za ta dauki sababbin mutane da ke sha’awa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

