DSS: Tukur Mamu Ya Karɓi N50m saga ’Yan Ta’addan da Suka Kai Hari Kaduna
- Wanda hukumar DSS ta gabatar a kotu ya shaida cewa Tukur Mamu ya karɓi N50m daga shugaban ƙungiyar masu 'yan ta'addan da suka kai hari Kaduna a 2022
- Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da Tukur Mamu bisa zargin karɓar fansa, mu'amala da kuɗin ta’addanci da kuma kawo cikas ga kwamitin CDS
- Shi ma wanda ake zargin ya shigar da ta shi karar, yana kalubalantar ayyana shi a matsayin 'dan ta'adda yayin da ake ci gaba da shari’arsa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – A ci gaban shari’ar da ake yi wa Tukur Mamu a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, an samu sababbin bayanai a kan harin da 'yan ta'adda suka kai wa matafiya a Kaduna.
Wani shaidan DSS ya bayyana cewa an samu Mamu da karɓar N50m daga wani mutum mai lakabin Shugaba, wanda ake zargin 'dan ta'adda ne.

Source: Facebook
Jaridar Legit ta wallafa cewa ana zargin Shugaba shi ne shugaban tawagar da ta kai harin jirgin kasa na Abuja–Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tuhumar Tukur Mamu da ta'addanci
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Tukur Mamu yana fuskantar tuhuma masu nauyi da suka haɗa da karɓar kuɗin fansa daga iyalan fasinjojin da aka sace.
Ana kuma zarginsa da mu’amala da kuɗin da ake zargin na ta’addanci ne da tarwatsa aikin kwamitin da Shugaban Ma’aikatan Tsaro (CDS) ya kafa don tattaunawa.
Haka kuma, ana zargin Tukur Mamu da musayar saƙonnin murya da kakakin Boko Haram, da sauran tuhume-tuhume.
A zaman kotun na ranar Talata, shaidan na shida daga DSS ya ce ƙungiyar ta’addancin ta bukaci Mamu ya koyar da su yadda ake bude shafin intanet domin gudanar da ayyukansu.
DSS ta kuma yi ikirarin cewa Tukur Mamu ya ba da shawara ga ’yan ta’adda da su tattauna kai tsaye da iyalan wadanda suka sace, maimakon bin kwamitin gwamnatin tarayya.
Tukur Mamu ya kai karar gwamnati
Shaidan ya bada wannan bayani ne yayin da yake fassara sautin tattaunawar Mamu da jami’an tsaro lokacin da aka kama shi a Masar kafin a dawo da shi Najeriya.
A gefe guda kuma, Tukur Mamu ya shigar da kara kan kare haƙƙinsa, inda yake kalubalantar ayyana shi a matsayin dan ta'adda da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya yi.

Source: UGC
Lauyansa ya yi ikirarin cewa tun da bai yanke masa hukunci ba har yanzu ana daukarsa a matsayin wanda ake zargi kawai ne kawai.
Alkalin kotun ya dage cigaban shari’ar zuwa 23 ga Fabrairu 2026, domin bangarorin da ke shari’a su gabatar da rubutattun muhawarar karshe a shari'ar.
Za a yi hakan ne bisa tanade-tanaden Sashe na 49 na Dokar Ta’addanci da Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Gwamnati ta kai Tukur Mamu kotu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnati ta gurfanar da Tukur Mamu gaban Mai shari’a Inyang Ekwo, domin ci gaba da sauraron tuhumar da ake masa kan alaka da ƙungiyoyin ’yan ta’adda.
Gwamnati ta yi ikirarin cewa ta tattara hujjoji masu karfi kan mutumin da aka ce ya taka rawa wajen sasanta batun fashin jirgin kasa na Abuja–Kaduna, har ma da sakin wasu da aka sace.
Hukumar DSS ta dage cewa tana bukatar ci gaba da rike Mamu har sai an tabbatar da dukkannin bayanan da suka shafi hulɗarsa da masu kai hare-hare da garkuwa da jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


