Sace Ɗalibai: Yadda Mahaifin Yara 3 da Aka Ɗauke Ya Mutu saboda Bugun Zuciya

Sace Ɗalibai: Yadda Mahaifin Yara 3 da Aka Ɗauke Ya Mutu saboda Bugun Zuciya

  • Kungiyar CAN a Arewacin Najeriya ta bayyana damuwa matuka bayan sace dalibai a makarantar coci a Nigeria
  • Shugaban CAN na Arewa, Rabaran John Hayab, ya ce sun yi rashin wani magidanci bayan sace 'ya'yansa har guda uku
  • Hayab ya bayyana cewa iyalai a Kebbi, Kwara da Niger na cikin tsananin tashin hankali, inda wasu yara suka tsere

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Shugaban CAN a Arewa da kuma Abuja, Rabaran John Hayab, ya bayyana damuwa game da ci gaba da tsare dalibai daga jihar Niger.

Hayab ya bayyana mutuwar wani uba sakamakon bugun zuciya bayan sace ’ya’yansa uku a makarantar St Mary’s.

Kungiyar CAN ta ce an rasa dattijo bayan sace 'ya'yansa 3
Kofar shiga makarantar katolika a Papiri da ke jihar Niger. Hoto: John Ayuba.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata hira da ya yi da jaridar ARISE News a jiya Talata 25 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

'Maganganun Tinubu ne suka jawo': Ministan Buhari kan karuwar rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da iyalan daliban ke ciki

Hayab ya ce iyalan da aka sace ’ya’yansu a Kebbi, Kwara da Niger suna fama da tashin hankali da radadi mai tsanani.

Ya bayyana cewa mutumin, wanda ake kira Mr Anthony, ya kasa jure tashin hankali, domin rashin yaran ya firgita shi ƙwarai har zuciyarsa ta samu matsala.

Hayab ya ce ba ya sukar gwamnati, amma yana bayyana gaskiya, domin matsalar na addabar iyaye, kuma yawancinsu suna tsoron magana saboda tsananin damuwa.

Ya kara da cewa iyayen yaran da aka sace a Niger sun shiga rudani, musamman ganin ba a san inda yaran suke ba ko halin da suke ciki, cewar Punch.

Yawan dalibai da suka tsere daga miyagu

Hayab ya nuna takaici saboda babu isasshen tsaro a yankin, yana mai jaddada cewa ’yan Najeriya na bukatar aiki, ba bayanai ba kawai.

Ya ce dalibai 50 sun tsere daga dajin bayan harin, amma fiye da 265 har yanzu ba a gansu ba, mafi yawansu ’yan shekaru tara zuwa 14.

Kara karanta wannan

"Akwai dalili": Hadimin Tinubu ya fadi abin da ya sa sojoji ba su iya farmakar 'yan bindiga

Ya bayyana farin ciki bayan wasu ’yan makarantar Maga 24 sun samu ’yanci, amma ya ce iyalai sun shiga mummunan yanayi saboda gazawar tsarin tsaro.

CAN a Arewa ta koka kan matsalar tsaro
Shugaban CAN a Niger da mashigar makarantar Katolika a Nigeria. Hoto: Catholic Broadcast Commission, Nigeria.
Source: Facebook

Fasto ya soki yanayin tsaro a Najeriya

Hayab ya ce Najeriya na da isasshen ma’aikatan tsaro, amma ba a amfani da su yadda ya kamata, domin da yawa suna tsaron manyan mutane maimakon kare talakawa.

Ya ce bankuna ya kamata su dauki jami'an tsaro na kansu, domin ’yan sanda da yawa sun makale suna tsaron su, abin da ke rage yawan jami’an tsaro ga jama’a.

Ya yaba da umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye ’yan sanda daga manyan mutane tare da neman a mayar da su sansanoni domin aiki.

Jerin sunayen dalibai, malamai da aka sace

Mun ba ku labarin cewa Cocin Katolika da ke garin Kwantagora ya saki sunayen duka malamai da daliban da 'yan bindiga suka sace a jihar Niger.

Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da kokarin ceto wadanda suka rage a hannun 'yan bindiga.

A makon jiya ne yan bindiga suka kai hari makarantar Katolika a jihar Niger, suka yi awon gaba da daruruwan dalibai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.