Sojoji Sun Yi wa 'Yan Ta'adda Ruwan Wuta da Suka Kutsa Dajin da Suka Buya

Sojoji Sun Yi wa 'Yan Ta'adda Ruwan Wuta da Suka Kutsa Dajin da Suka Buya

  • Sojojin Najeriya sun kaddamar da wani gagarumin farmaki da fatattakar ‘yan ta’adda a dazuzzukan Kudancin Taraba
  • Farmakin ya faru ne bayan hare-haren da ake zargin makiyaya masu dauke da makamai ke kai wa al’ummomi a yankin
  • Rahoto ya ce manoma za su samu damar kwashe amfanin gona da suka yi niyyar cirewa kafin bikin karshen shekara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba - Rundunar sojin Najeriya ta kara zafafa hare-hare kan miyagun da ke ɓoye a dazukan Kudancin Taraba.

Wannan yunkuri ya biyo bayan matsin lamba da harin da ake zargin wasu makiyaya masu makamai ke kai wa al’ummomin yankin Donga.

Dakarun sojojin Najeriya a Taraba
Wasu dakarun Najeriya ta farautar 'yan ta'adda a Taraba. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa sojojin sun shiga dazukan Zambana da kauyen Ayu domin kakkabe ‘yan ta’adda bayan rahotannin barazanar tsaro da ta tilasta wa mazauna yankin tserewa.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Tinubu ya ba sojoji umarnin mamaye dazuzzuka a Kwara da jihohi 2

A yayin aikin, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan tare da tilasta musu guduwa, lamarin da ya kara raunana karfin su na kai hari ko tsayawa a yankin.

Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda a Taraba

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa sojoji sun yi arangama da ‘yan ta’addan inda suka yi amfani da karfin yaki na zamani wajen murkushe su.

Majiyar ta ce sojojin sun fatattaki tawagar ta hanyar kai musu farmaki mai munin gaske wanda ya tarwatsa tsare-tsaren su gaba ɗaya.

“Ayyukan da aka gudanar cikin tsari da hanzari sun raunana karfin ‘yan ta’addan sosai, tare da tilasta musu kaura daga maboyar da suka dade suna zama.”

- Inji majiyar

A cewar majiyar, wannan aikin ya bai wa manoma damar kwashe amfanin gonakinsu cikin kariya bayan tsawon lokaci suna cikin fargaba da tsoron hare-hare.

Sakon kwamandar rundunar sojojin

Kwamandan rundunar, Birgediya Janar Uwa, ya ce rundunar ta kuduri aniyar ci gaba da tsaurara matakan tsaro a yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, Boko Haram sun guntule kan mata saboda zargin tsafi

Ya bayyyana cewa za su cigaba da tabbatar da tsaro musamman yayin da ake tunkarar bukukuwan karshen shekara.

Yadda sojoji suka shiga dajin Taraba
Wasu dakarun Najeriya a cikin dajin Taraba. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Birgediya Janar Uwa ya ce sojojin za su ci gaba da mamaye dukkan wuraren da ake zargin ‘yan ta’adda na ɓoye, tare da hana su samun damar sake yunƙurin kawo barazana ga al’ummar yankin.

Ya kara da cewa:

“Mun kuduri aniyar ci gaba da matsa lamba kan wadannan miyagun mutane domin dawo da zaman lafiya a kowane yankin da abin ya shafa.”

Rahotanni sun nuna cewa aiki na cikin jerin matakan da Operation Zafin Wuta ke dauka domin kawar da ‘yan ta’adda da ke haddasa kashe-kashe, tayar da tarzoma da lalata gonaki.

Tsaro: Doguwa ya nemi rufe majalisa

A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar wakilai daga Kano, Alhassan Ado Doguwa ya yi magana mai zafi game da rashin tsaro.

Hon. Ado Doguwa ya ce lokacin shiru da zuba ido ana kashe mutane a sassan Najeriya ya wuce, yana cewa dole a dauki mataki.

Kara karanta wannan

An kama 'dan bindigan da ya gudu Bauchi daga Zamfara da makamai da kudi

A korafin da ya yi, ya yi kira da a rufe majalisar wakilai har sai a shawo kan matsalar tsaro da ta addabi miliyoyin 'yan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng