Ana so a Rika Hukunta Jami'an Gwamnati da ke Tattaunawa da 'Yan Bindiga
- Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya ba da shawarar hukunta duk wani jami’in gwamnati da ya ba masu garkuwa kudin fansa
- Hon. Benjamin Kalu ya ce yin hakan cikin watanni shida masu zuwa zai taimaka wajen dakile ta’addanci da karfafa tsarin shari’a
- Kalu ya nemi samar da dokar hana tattaunawa da ’yan bindiga, da karfafa ’yan sanda, da kuma hanzarta tsarin kafa ’yan sandan jiha
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A wani zaman musamman da majalisar wakilai ta gudanar kan tsaro, Benjamin Kalu ya gabatar da shawara mai tsauri kan yadda gwamnati ke tunkarar matsalar garkuwa da mutane.
Ben Kalu ya nemi majalisa ta ayyana hukunci ga jami’an gwamnati da ke shiga tattaunawa da ’yan bindiga da biyan kudin fansa.

Source: Twitter
Rahoton Channels TV ya ce Kalu ya bayyana cewa matsalar tsaro ta kai wani hali da ya kamata a dauki matakai cikin gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya fadi haka ne bisa la’akari da yadda hare-haren da garkuwa da mutane suka karu a makwannin baya-bayan nan.
A na son daina sulhu da 'yan bindiga
A cewar Kalu, dokar da ya gabatar za ta zama bangare na muhimmiyar manhajar aikin majalisa a tsakanin yanzu da wata shida masu zuwa.
Kalu ya jaddada cewa dole majalisa ta kafa dokar da za ta “haramta tattaunawa da ’yan bindiga” tare da hukunta kowane jami’in gwamnati da ya shiga irin wadannan yarjejeniya ba bisa ka’ida ba.

Source: Facebook
Ya bayyana muhimmancin tursasa bin tsarin shari’a, yana cewa:
“Abin da muke bukata shi ne hana duk wata tattaunawa da masu laifi, da tilasta aiwatar da tsarin shari’ar laifuffuka maimakon shirye-shiryen afuwa marasa tsari.”
Ya kara da cewa dole ne a tabbatar da gurfanar da duk wanda aka kama da zargin ta’addanci ko garkuwa da mutane.
Bukatar inganta aikin ’yan sanda
Kalu ya yi kira ga gwamnati ta kara karfafawa jami’an tsaro gwiwa ta hanyar inganta kayan aiki, musamman na zamani.
Ya ce wannan zai taimaka wa rundunar ’yan sanda wajen fuskantar manyan kalubalen tsaro:
“Rundunar ’yan sanda da ba za ta iya tsara abin da ke gaban ta fiye da albashin wata mai zuwa ba, ba za ta iya kare kasar nan ba.”
Kalu ya ce lokaci ya yi da za a hanzarta tattaunawa kan kafa ’yan sandan jiha ko na kananan hukumomi domin kara kusantar da tsaro ga al’umma.
Me ya sa 'yan ta'adda ke kara karfi?
Hon. Kalu ya yi Allah-wadai da tsarin da wasu hukumomi ke bi na tattaunawa da ’yan bindiga duk da cewa dokar kasa ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ko kisa ga masu garkuwa da mutane.
A bidiyon da ya wallafa a X, Kalu ya ce irin wadannan yarjejeniyoyi na sa kungiyoyin ta’addanci kara karfi:
“Yarjejeniyar afuwa da tattaunawa marasa tsari suna karfafa wadannan kungiyoyi.”
Ado Doguwa ya nemi a rufe majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya ce matsalar tsaro ta yi kamari a Najeriya.
Hon. Ado Doguwa ya ce ya kamata a rufe majalisar wakilai domin mayar da hankali game da matsalar tsaro.
A martanin da mataimakin majalisar ya yi wa Doguwa, Benjamin Kalu ya ce bai goyi bayan rufe majalisar ba sam-sam.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


