Asiri Ya Fara Tonuwa: Dan Bindiga Ya Fadi Yadda Aka Ceto Daliban Kebbi 25

Asiri Ya Fara Tonuwa: Dan Bindiga Ya Fadi Yadda Aka Ceto Daliban Kebbi 25

  • An tabbatar da cewa an ceto dalibai mata 25 da aka sace a Maga a jihar Kebbi, lamarin da ya jawo mahawara a kafafen sada zumunta
  • Bidiyon da ya fito daga hannun dan bindiga ya nuna yadda aka kula da yaran, tare da bayyana cewa sulhu da tattaunawa ne ya ba da damar sakinsu
  • A cikin bidiyon, dan ta’addan ya tabbatar cewa ba su cutar da yaran ba, yana mai cewa gwamnati ta kasa karbarsu da karfi, sai da aka cimma maslaha

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi, Kebbi - A jiya Talata 25 ga watan Nuwambar 2025 aka yi nasarar ceto dalibai 25 da aka sace a jihar Kebbi.

Mutane da dama sun yi ta tambayar hanyar da aka yi aka kwato daliban duba da irin daukar hankali da lamarin ya yi.

Kara karanta wannan

'Tinubu ne ya tsara komai': Yadda aka ceto Kiristoci 38 da aka sace a Kwara

An 'gano' yadda aka ceto daliban jihar Kebbi
Shugaba Bola Tinubu da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

Daliban Kebbi: Yan bindiga sun saki bidiyo

Wani mai amfani da shafin X, @AM_Saleeeem ya wallafa wani bidiyon dan ta'adda na bayanin yadda aka ceto yaran daga gare su.

A cikin bidyon, an gano dan ta'addan yana yi wa yaran tambayoyi game da yadda suka kula da su ba tare da matsala ba.

Ya kuma tabbatar da cewa sun tattauna ne da wasu manyan mutane a Najeriya wanda ya yi nasarar ceto yaran daga hannun yan bindigar.

Ga abin da yake fada a bidiyon:

"An bar ku da yunwa? Yaran suka amsa da a'a, an baku kulawa? suka ce eh, To in sha Allahu kun ga dai za a mayar da ku ga iyayenku da yardar Allah, akwai wacce aka yi wa maganar banza daga cikinku? suka ce babu.
"To za a bayar da ku bisa sulhu domin zaman lafiya, ku koma lafiya, karfi bai amshe ku ba, jirgi nawa ya taho nan?

Kara karanta wannan

Ana neman daliban Kebbi, 'yan sanda sun ceto mata 25 da aka yi garkuwa da su

Suka ce ba su san iyaka ba.

"Kun ga dai gwamnati ta kasa amsar ku ko, an zo za a karbe ku bayan tattaunawa da magana da manya."
Ana ta maganganu kan yadda aka ceto daliban Kebbi daga yan bindiga
Taswirar jihar Kebbi da aka sace dalibai har guda 25 a makon jiya. Hoto: Legit.
Source: Original

Maganganu da ya biyo bayan ceto dalibai

Tun farko, yan Najeriya da dama na kokwanton yadda aka yi aka ceto daliban tare da tambayar shin ko an biya kudin fansa? sannan ya aka kare da yan biindigar bayan ceto yaran?

Daga bisani, gwamnatin jihar Kebbi ta ce ko sisin kwabo ba a biya game da ceto su amma ba ta yi karin haske hanyar da aka bi ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Dubban dalibai da aka sace tun 2014

Mun kawo muku rahoto kan yawan dalibai da aka yi garkuwa da su a Arewacin Najeriya tun a zamanin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Rahotanni sun nuna hare-haren ’yan bindiga sun shafi dubban dalibai cikin shekaru 11 da wanda ya tayar da hankula musamman sace-sacen Niger da Kebbi wanda suka tunzura jama’a.

Kara karanta wannan

'Na gaza': Sanata a Kebbi ya yi nadamar alkawari ga 'yan mazabarsa lokacin zabe

Sababbin hare-haren makarantu sun haifar da tsoro a tsakanin dalibai da iyayen yara bayan dauke dalibai 303 daga makarantar cocin Katolika a Niger; kwana biyar kacal bayan sace dalibai 25 a Jihar Kebbi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.