Bincike: Ƴan Sanda Sun Bayyana Wadanda Ake Zargi da Sace Mutane 10 a Jihar Kwara

Bincike: Ƴan Sanda Sun Bayyana Wadanda Ake Zargi da Sace Mutane 10 a Jihar Kwara

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da harin da aka kai garin Isapa, tare da fara aikin ceto mutanen da aka sace
  • Kwamishinan ’yan sanda ya kai ziyara Isapa domin tantance al’amura, inda ya ce an dauki matakai na kubutar da mutanen
  • 'Yan bindiga dauke da makamai ne suka kai har Isapa, inda suka sace manya da yara, ciki har da mata masu juna biyu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Rundunar ’yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da faruwar wani mummunan harin 'yan bindiga a Isapa, kusa da Obbo-Ile, a ranar Litinin.

A yayin wannan harin, 'yan sandan sun ce miyagun sun yi garkuwa da mutane 10 kuma sun tsere da su zuwa cikin daji.

Rundunar 'yan sanda ta fitar da rahoton farko game da harin 'yan bindiga a Kwara
Babban sufetan 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun yana aiki a ofis. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ta fitar, a cewar rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Bayan ceto dalibai 25, shaidanin ɗan bindiga ya shiga hannun jami'an tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton 'yan sanda kan sace mutane a Kwara

Sanarwar ta ce ’yan sanda tare da 'yan sa-kai sun dukufa wajen bincike da aikin ceto, yayin da aka sa kauyen ƙarƙashin tsattsauran tsaro.

"Da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Litinin ne 'yan sanda suka samu rahoton harbe-harbe a yankin Isapa, inda aka tura jami’ai cikin gaggawa domin dakile lamarin.
"Rahoton farko ya nuna cewa wasu mutane dauke da makamai, da ake zargin makiyaya ne, suka farmaki kauyen tare da bude wuta kan mai uwa da wabi."

- SP Adetoun Ejire-Adeyemi.

Sanarwar ta ce an sace mutane 10 a yayin harin, kuma yanzu haka jami'ai suna sintiri a dazuzzuka da yankunan da ke kewaye da kauyen domin ganin an ceto mutanen da cafke masu laifin.

Kwamishinan 'yan sanda ya kai ziyara

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kwara, CP Adekimi Ojo, ya je Isapa domin tabbatar da hakikanin halin da ake ciki, in ji rahoton

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: 'Yan bindiga sun shiga jihar Kano, sun yi garkuwa da mata

A yayin ziyarar, ya gana da sarakuna da shugabannin al’umma, ciki har da Onisapa na Isapa, Oba Gbenga Adeyeye, da Olokesa na Okesa, Oba Fagbamila Raphael Olusegun.

Ya tabbatar musu da cewa rundunar ’yan sanda za ta ƙara kaimi wajen ganin an ceto mutanen da aka sace.

Wani jagoran al’umma ya tabbatar da cewa bakwai daga cikin mutanen da aka sace ’yan gida daya ne, ciki har da mata masu juna biyu, mata masu shayarwa da kananan yara.

An rahoto cewa 'yan bindigar sun sace mutane da dama ciki har da mata masu shayarwa
Taswirar jihar Kwara da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sunayen mutanen da aka sace a Kwara

Sun ce mutanen da aka sace sun haɗa da Talatu Kabiru mai shekara 20, Magaji mai shekara shida, Kande mai shekara biyar, Hadiza mai shekara 10, da Mariam mai shekara shida.

Sauran da aka sa sun hada da Saima mai shekara biyar, da mata biyu Habibat da Fatima Yusufu, wadda ita ce mai juna biyun.

Sannan akwai Sarah Sunday mai shekara 22, Lami Fidelis mai shekara 23 wadda ke shayarwa, da Haja Na Allah, wadda ita ma mai juna biyu ce.

'Yan bindiga sun sace masu ibada a Kwara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin rashin imani a Kwara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan ta'adda sun farmaki cocin Christ Apostolic Church (CAC), Oke Isegun da ke karamar hukumar Ekiti, jihar Kwara.

Rahoton farko ya nuna cewa miyagun sun bude wuta kan mai uwa da wabi, inda suka kashe fasto tare da yin garkuwa da masu ibada da dama.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Adekimi Ojo ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da yin karin bayanin halin da ake ciki da matakan da aka dauka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com