'Zubar da Jini Ya Yi Yawa,' Ado Doguwa Ya Nemi a Rufe Majalisar Wakilan Najeriya

'Zubar da Jini Ya Yi Yawa,' Ado Doguwa Ya Nemi a Rufe Majalisar Wakilan Najeriya

  • Hon. Alhassan Ado Doguwa ya nemi daukar matakan gaggawa a majalisa saboda matsalar tsaro da ya ce ta yi tsanani
  • Ya jaddada cewa kashe-kashe, garkuwa da mutane da hare-hare sun kai matakin da bai kamata majalisa ta ci gaba da aiki ba
  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya ce yana da ja a kan maganar da Ado Doguwa ya yi a lokacin da ya masa martani

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Zaman da majalisar wakilai ta yi a kan tsaro ya dauki zafi a lokacin da Alhassan Ado Doguwa, dan majalisa mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada daga jihar Kano, ya yi magana.

A yayin muhawarar da aka yi, Hon. Ado Doguwa ya bukaci a dakatar da ayyukan majalisa na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Ana so a rika hukunta jami'an gwamnati da ke tattaunawa da 'yan bindiga

Hon. Alhassan Ado Doguwa
Ado Doguwa yayin da ya ke bayani a majalisa. Hoto: House of Representaives, Federal Republic of Nigeria
Source: Facebook

Rahoton Premium Times ya ce Hon. Doguwa ya nemi a ayyana dokar ta-baci domin ba wa batun tsaro muhimmanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ado Doguwa ya nemi a rufe majalisa

Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa lamuran tsaro sun kai wani mataki mai tayar da hankali, inda ya ce:

“Shugaba, za mu iya ayyana dokar ta-baci a majalisa. A rufe majalisar gaba ɗaya. Wace irin doka muke yi alhali ana zubar da jini a kasar nan, jama'a suna ta kuka?”

Ya kara da cewa al’ummar da suke wakilta suna cikin mawuyacin hali, kuma majalisar ba za ta ci gaba da zama ba tamkar babu komai.

Doguwa ya bayyana cewa an rusa kauyuka da dama musamman a Arewacin Najeriya ta hanyar hare-hare.

Ya kara da cewa manoma ba sa iya zuwa gonaki kuma ’yan kasuwa ba sa iya zuwa cik kasuwa cikin kwanciyar hankali.

Kiran daukar mataki na musamman

Doguwa ya bukaci majalisar ta dakatar da ayyuka ta mayar da hankali kan daukar matakai na musamman.

Kara karanta wannan

'Ana cikin tsoro,' 'Yan majalisar sun yi zazzafar muhawara kan rashin tsaro

Ya nemi karin hadin kai da al’ummomin yankuna ta hanyar tallafawa kungiyoyin sa-kai da sake tsara su domin karfafa tsaron kasa.

Alhassan Ado Doguwa a majalisa
Dan majalisar wakilai, Hon. Ado Doguwa. Hoto: Alhassan Ado Doguwa
Source: UGC

Ya bada misalin ziyara da suka kai jihar Kebbi tare da shugaban majalisa, inda ya ce ya ga gwamnoni a cikin tsananin damuwa:

“Na ga gwamna yana kukan zuci.”

Ya jaddada cewa matsalar tsaro tana da tasiri kai tsaye a rayuwar jama’a — manoma, ’yan kasuwa, da masu ibada.

Martanin majalisa ga Ado Doguwa

Mataimakin shugaban majalisa, Benjamin Kalu, ya ce duk da cewa matsalar ta yi tsanani, rufe majalisa ba mafita ba ne.

Vanguard ta rahoto ya ce:

“Mu ne 'yan Najeriya suka zuba wa ido. Ba za mu rufe majalisa ba. Za mu tsaya a nan mu nemo mafita tare.”

Boko Haram sun kashe mata a Borno

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe mata a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun kashe matan ne ta hanyar fille musu kawuna saboda zarginsu da sihiri.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya gyarawa shugabannin Arewa zama kan rufe makarantu

Bayan kashe matan, mayakan sun gargadi mutanen yankin da su rika bin dokokin da suka sanya kuma su guji neman tserewa wasu wurare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng