Rufe Makarantu: Wike Ya Dakatar da Sakataren Ilimi a Abuja, Danlami Hayyo

Rufe Makarantu: Wike Ya Dakatar da Sakataren Ilimi a Abuja, Danlami Hayyo

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya fusata game da fitar da wata sanarwa a birnin da ya shafi rufe makarantu saboda rashin bin ka'ida
  • Hakan ya jawo dakatar da sakataren ilimi, Danlami Hayyo saboda rahoton kulle makarantu ba tare da izinin ministan harkokin Abuja ba
  • Hukumar FCTA ta karyata sanarwar cewa za a rufe makarantu a ranar 28 ga Nuwamba, ta ce ba a taba yanke irin wannan hukunci ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Yada labarin rufe makarantu a Abuja saboda fargabar ta'addanci ya fusata Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Wike ya dakatar da Danlami Hayyo wanda shi ne sakataren ilimi na Abuja, bayan yaduwar rahoton cewa an umurci rufe dukan makarantu.

Wike ya karyata labarin rufe makarantu a Abuja
Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta samu wannan bayani daga shafin hadimin ministan Abuja, Lere Olayinka da ya wallafa a Facebook kan sanarwar da ta ce za a kulle nakarantun birnin tarayya a ranar 28 ga Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

'Ana cikin tsoro,' 'Yan majalisar sun yi zazzafar muhawara kan rashin tsaro

Sanarwar da ta yada rufe makarantu a Abuja

A baya dai an ga wata takarda da aka sanya wa hannu, wacce ta umarci duk makarantun sakandare na gwamnati su dakatar da karatu kafin ko ranar 28 ga Nuwamba saboda tsaro.

Takardar ta ce a dakatar da dukkan ayyukan makarantu nan take, tare da tabbatar da cewa dalibai sun watse cikin natsuwa da tsaron lafiyarsu ba tare da tashin hankali ba.

Wannan labarin da aka yada ya fusata Wike duba da cewa ba a nemi izini ba kafin fitar da sanarwar da ke da matukar muhimmanci.

Wike ya dakatar da sakataren ilimi a Abuja
Minista Nyesom Wike da sakataren ilimi a Abuja. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Facebook

Martanin Wike kan sanarwar rufe makaranutu

Sai dai daga baya, Lere Olayinka, mai magana da yawun ministan, ya karyata batun, inda ya ce ba a taba yanke irin wannan hukunci ba a matakin gwamnati.

Olayinka ya ce an umurci shugabar ma’aikatan Abuja, Nancy Sabanti Nathan, da ta dauki matakin ladabtarwa kan Aishatu Sani Alhassan bisa ka’idojin aikin gwamnati.

Ya bayyana labarin kulle makarantu a matsayin “karya da yaudara”, yana mai gargadin iyaye, dalibai da shugabannin makarantu da su yi watsi da jita-jitar.

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: Gwamnatin Gombe ta sanar da ranar rufe makarantu

Sanarwar ta ce jadawalin karatu na shekara bai canza ba, kuma makarantu za su ci gaba da aiki yadda aka tsara tun farko ba tare da tangarda ba.

Hukumomi a Abuja sun kara tabbatar da cewa an dauki matakan tsaro na musamman domin kare dalibai da mazauna yankin gaba daya.

Olayinka ya ce ministan ya bayar da umarnin dawo da Operation Sweep da sauran dabarun tsaro domin karfafa tsaron makarantu da al’ummomi.

Wike ya gindaya sharadin zaman lafiya a PDP

Mun ba ku labarin cewa wani jigon PDP, Umar Sani ya ce Nyesom Wike ya bukaci jam'iyyar da ta hakura da takarar shugabancin kasa a 2027.

A cewar Umar, hakura da takarar ne sharadin sulhu da ministan Abuja ya ba PDP, tare da barazanar sake jefa ta a rikici.

Jigon ya kuma yi magana game da rashin halartar jihohin Rivers, Osun da Taraba babban taron PDP da aka gudanar wanda aka yi a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.