Bayan Ceto Dalibai 25, Shaidanin Ɗan Bindiga Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro

Bayan Ceto Dalibai 25, Shaidanin Ɗan Bindiga Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro

  • Jami’an tsaro sun samu nasara kan yan ta'adda bayan cafke daya daga cikin hatsabiban masu garkuwa da mutane da ya kai hare-hare
  • Majiyoyi sun tabbatar da kama fitaccen dillalin makamai ga ’yan bindiga da ake kira “Gwandara 01”, bayan sahihin bayanan leƙen asiri
  • Bincike ya danganta shi da garkuwa da mutane a Garam da Bwari, ciki har da sace babban Fasto a 2024, ana farautar sauran ’yan kungiyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dubun shedanin dan bindiga ya cika bayan jami'an tsaro sun yi ram da shi a birnin Abuja wanda ake ganin zai rage tasirin maharan a yankin.

An ce jami’an tsaro sun kama mashahurin mai garkuwa da mutane kuma babban mai samar da kayan aiki ga ’yan bindiga da suke sheke ayarsu a birnin da kewaye.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, Boko Haram sun guntule kan mata saboda zargin tsafi

Sojoji sun kama fitaccen dan bindiga a Abuja
Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Defence Headquaters Nigeria.
Source: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya ce Yau Ibrahim Dauda, wanda aka fi sani da “Gwandara 01” ya shiga hannu bayan samun bayanan sirri daga al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka ceto dalibai 25 daga jihar Kebbi

Wannan nasara da jami'an tsaro suka samu ya zo a daidai lokacin da ake farin cikin ceto dalibai 25 da aka sace su a jihar Kebbi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa dalibai sun shaki iskar 'yanci ne a yau Talata 25 ga watan Nuwambar 2025 bayan shafe mako daya a hannun 'yan bindiga.

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da ceto yaran a wani da Bayo Onanuga ya wallafa a X inda aka gano su a cikin bas bayan dauko su lamarin da ya jefa shakku da tambayoyi kan yadda aka kubutar da su.

Jami'an tsaro sun cafke fitaccen dan bindiga a Abuja
Taswirar birnin Abuja da ke tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Fitaccen dan bindiga ya shiga hannu

Rahotanni sun bayyana cewa an cafke hatsabibin ne da taimakon rundunar Scorpion Squad misalin ƙarfe 5:40 na yamma a Bwari, bayan sahihan bayanan leƙen asiri.

Kara karanta wannan

"Akwai dalili": Hadimin Tinubu ya fadi abin da ya sa sojoji ba su iya farmakar 'yan bindiga

Majiyoyi sun ce Dauda yana cikin jerin wadanda ake nema saboda zargin jagorantar manyan hare-haren sace mutane a Abuja, musamman yankin Bwari daga 2024 zuwa yanzu.

Bincike ya danganta shi da garkuwa da mutane da dama a Garam Tafa da Bwari, ciki har da sace Fasto a 2024 a rukunin gidajen El-Rufai a kusa da makarantar lauyoyi

Majiyoyin sun bayyana cewa ana ci gaba da neman sauran yan ta'addar da suka tsere, domin cafke su da kwato makaman da suke amfani da su wajen aikata laifi.

An hallaka mahaifin dan bindiga a Katsina

Kun ji cewa tsautsayi ya sa an kashe Ibrahim Nagode, mahaifin shahararren dan bindiga “Fada”, a karamar hukumar Malumfashi, abin da ya jefa mutane a tashin hankali.

Hukumar DSS ta kama duka jami’an CJTF da suka fita aikin da ya jawo aka harbe Nagode har lahira wanda ya sanya tsoro a zukatan al'ummar yankin duba da halin da ake ciki.

Masana sun nuna fargaba cewa kashe mahaifin dan bindiga Fada bayan an yi sulhu na iya jawo hare-haren ramuwar gayya wanda ba dole lamarin ya yi dadi ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.