A Karshe, an Ceto Ɗalibai 25 da Ƴan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Su a Kebbi

A Karshe, an Ceto Ɗalibai 25 da Ƴan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Su a Kebbi

  • Daliban da aka sace a Kebbi sun kubuta, kuma majiyoyi sun tabbatar da ceto ɗalibai mata 25 da aka sace a makon jiya
  • Gwamnati ta tura dakarun haɗin gwiwa, ciki har da sojoji, ‘yan sanda da ‘yan sa-kai, domin bincike da nemo sauran daliban
  • Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da ceto daliban da aka sace a makon jiya inda ta yi karin haske kan jita-jitar biyan kudin fansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi, Kebbi - Rahotanni sun tabbatar mana da cewa daliban da aka sace a jihar Kebbi sun kubuta.

Majiyoyi sun ce an ceto ɗalibai mata guda 25 da aka sace daga makarantar mata da ke Maga da ke jihar.

An tabbatar da cewa an ceto daliban Kebbi 24
Taswirar jihar Kebbi da aka sace mata dalibai 25. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Leadership ya tabbatar da cewa an samu bayanin hakan ne daga majiya mai tushe a ranar Talata 25 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Daga Chibok, Kankara zuwa Maga: Dubban dalibai da aka sace tun daga 2014 a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace dalibai mata a Kebbi

A ranar 17 ga Nuwambar 2025, ‘yan bindiga sun kai hari makarantar, inda suka dauke dalibai mata 25, suka kashe ma’aikaci sannan suka jikkata wani jami’in tsaro.

A cewar rahoton Legit Hausa, dalibai biyu sun tsere daga hannun masu garkuwa, shugaban karamar hukumar Danko Wasagu ya ce yaran sun arce ne a lokacin da ake tafiya cikin daji, suka tsallake gonaki suka kubuta.

A ranar 19 ga Nuwambar 2025, shugaban Karamar Hukumar, Hussaini Aliyu, ya fitar da jerin sunayen daliban da aka sace, bisa rabawa aji-aji.

Martanin kwamshinan yan sanda a Kebbi

Bayan harin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Bello Sani, ya ce an tura karin jami’an tsaro, sojoji da ‘yan sa-kai domin nemo daliban.

Sani ya ce tawagar hadin gwiwa na bincike tare da duba dukkan hanyoyin da ake zargin masu garkuwa za su bi, da gandun dajin da ke kusa domin ceto yaran da kama barayin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta yi magana kan sace dalibai a Kebbi da Neja

Majiyoyi sun tabbatar da ceto dalibai 25 a Kebbi
Motar GGSS Maga da 'yan bindiga suka sace dalibai. Hoto: Amnesty International|Zagazola Makama.
Source: Facebook

Ana tambayar yadda aka ceto daliban Kebbi

Rahoton TheCable ya tabbatar da samun labarain ceto daliban da aka yi a yau Talata 25 ga watan Nuwambar 2025.

Ba a bayyana yadda aka yi nasarar ceto su, domin har yanzu babu ciakkun bayanai, amma ana sa ran gwamnati za ta fitar da sanarwa daga baya a daren nan.

'Yan Najeriya na ci gaba da jefa tambayoyi kan yadda aka yi aka ceto daliban yayin da suke tambayar yadda aka yi yan bindigar.

Abin gwamnatin Kebbi ta ce kan kudin fansa

Wasu sun nuna shakku game da hakan, dama tuni sun bayyana sace yaran a matsayin shirin wasan kwaikwayo duba da yadda lamarin ke tafiya.

Daga bisani, gwamnatin jihar Kebbi ta karyata cewa an biya kudin fansa kafin nasarar ceto daliban da aka sace.

Vanguard ta ruwaito gwamnatin na cewa ko sisin kwabo ba a ba yan bindiga ba kafin suka sake yaran da aka sace.

Kara karanta wannan

'Tinubu ne ya tsara komai': Yadda aka ceto Kiristoci 38 da aka sace a Kwara

Matawalle ya magantu kan daliban Niger

A baya, an ji cewa Bello Matawalle ya bayyana cewa an samu ci gaba matuka a kokarin ceto daliban makarantar da 'yan bindiga suka sace a Niger.

Karamin ministan tsaron ya ce an tura dakarun sojoji zuwa iyakoki da hanyoyin da 'yan bindiga ke bi a tsakanin Kebbi, Zamfara da Niger.

Dalibai mata kusan 25 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su, amma daga bisani daya daga ciki ta gudo kuma ta koma gida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.