Lamari Ya Girma: Gwamna Ya Rufe Ofishin Yakin Neman Zaben Tinubu, Ya Yi Gargadi
- Yayin da aka soma hangen zaben shekarar 2027, Gwamnatin Abia ta kawo tsaiko game da yakin neman zaben Bola Tinubu a jihar
- An rufe ofishin yakin neman zaben 'Renewed Hope Partners' na Shugaba Tinubu a Umuahia, inda jami’in RHP ya ce ba a basu sanarwa ba
- Rahoto ya nuna cewa duk kokarin neman ƙarin bayani daga lambobin da aka makala kan ginin ya ci tura, domin wayoyin ba su samuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Gwamnatin jihar Abia ta rufe wani ofishin yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu a birnin Umuahia.
Gwamnatin Abia ta rufe ofishin 'Renewed Hope Partners' na Shugaba Bola Tinubu da ke kan titin Ojike saboda saba ka'ida da aka yi.

Source: Twitter
An rufe ofishin kamfen Tinubu a Abia
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa kungiyar wata kungiya ce da ke tallata tsarin siyasar Tinubu a yankin Kudu maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta kasance karkashin jagorancin mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Kalu wanda ke ci gaba da bayyana ayyukan da Tinubu ga al'ummarsa.
Wani jami’in kungiyar RHP ya ce ya iso wurin aiki da safe sannan ya tarar da ofishin an rufe shi, babu wani gargadi ko sanarwa daga gwamnati.
Hukuncin da ke jiran masu saba doka
Sanarwar da Ma’aikatar Filaye da Gidaje ta liƙa a jikin ginin ta ce mallakar ginin ta karya sassan 41 da 100 na dokar harajin jihar ta 2020.
Takardar ta gargadi cewa duk wanda ya yi yunkurin cire hatimin ko kokarin yin wani abu da ya saba ka'ida, zai kasance cikin masu karya dokar haraji ta jihar.
An ce duk ƙoƙarin kiran lambobin da ma’aikatar ta bayar domin karin bayani ya gagara, domin wayoyin ba su samuwa lokacin da aka bayyana rahoton.

Source: Original
Gargadin da gwamnatin Abia ta yi ga al'umma
A sanarwar da aka manna, an gargadi al'umma da ka da su kuskura su yi kokarin bude ofishin inda ta ce hakan saba doka ne.
Sanarwar:
“Ma’aikatar Filaye da Gidaje, wannan ginin ya saba wa Sashe na 41 da 100 na Dokar Harajin Jihar Abia (Tattarawa da Haɗa Dokoki), Doka Mai Lamba 7 ta 2020, don haka an rufe shi.
“Duk wanda ya yi ƙoƙarin buɗe wannan gini har da mai gidan, maƙwabci ko mai wucewa ya sabawa Dokar Haraji ta Jihar Abia Lamba 7 ta 2020, A yi hattara, ka da a kusanto shi.”
An ruguza ofishin kamfen Tinubu a Benue
A baya, mun ba ku labarin cewa Hukumar raya birane ta jihar Benue ta rusa wani bangare na ofishin yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu da ke birnin Makurdi.
Masu goyon bayan Tinubu sun bayyana hakan a matsayin mataki maras hujja, suna masu cewa su na da lasisin mallakar filin yayin da lamarin ya kusa komawa rigima.
Gwamnatin jihar Benue ta musanta cewa siyasa ce ta haddasa hakan, ta kuma bayyana dalilin daukar matakin rusa ofishin wanda ya sha bamban da maganar siyasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

