Sulhu Zai Lalace: Jami'in Tsaro Ya Kashe Mahaifin Rikakken Dan Bindiga a Katsina

Sulhu Zai Lalace: Jami'in Tsaro Ya Kashe Mahaifin Rikakken Dan Bindiga a Katsina

  • An kashe Ibrahim Nagode, mahaifin shahararren dan bindiga “Fada”, a Malumfashi, abin da ya jefa mutane a tashin hankali
  • Hukumar DSS ta kama duka jami’an CJTF da suka fita aikin da ya jawo aka harbe Nagode har lahira, a cewar rahotanni
  • Masana sun nuna fargaba cewa kashe mahaifin dan bindiga Fada bayan an yi sulhu na iya jawo hare-haren ramuwar gayya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - An shiga tashin hankali a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina bayan wani jami'in CJTF ya harbe Alhaji Ibrahim Nagode har lahira.

Alhaji Ibrahim Nagode, mai shekara 60, wanda ke zaune a garin Na’alma ya kasance mahaifin rikakken dan bindiga, Haruna Ibrahim, watau Fada.

Jami'an tsaro sun kashe mahaifin hatsabibin dan bindiga a Katsina.
Jihar Katsina, inda aka yi sulhu da 'yan bindiga a wasu garuruwa Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe mahaifin dan bindiga a Katsina

Wani rahoto na Zagazola Makama da ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa jami'in rundunar hadin gwiwar tsaro ta farar hula ya kashe Alhaji Nagode bayan an yi sulhu a yankin.

Kara karanta wannan

Amarya ta kashe ango a 'wani yanayi' bayan kwana 3 da daura masu aure a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotan ya nuna cewa an harbi Nagode ne yayin da ɗansa Fada ya dawo yankin, sakamakon sabuwar yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin al’ummomi da ’yan bindiga a yankin.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne bayan hukumomin tsaro sun samu rahoton sirri cewa wasu 'yan bindiga na taruwa domin kai hari a yankin.

An ce jami'an tsaron na CJTF sun saka yankin cikin tsauraran matakan sintiri bisa wadannan bayanan sirri da suka samu, don dakile duk wata barazana.

DSS ta cafke jami'an CJTF da suka yi harbi

Wani jami’in tsaro ya ce an aika da dakarun CJTF yankin domin hana sake barkewar rikici, amma abin ya rikide zuwa rikici, da ya jawo har aka harbe Nagode har lahira.

Jami'in ya bayyana cewa yanzu haka yankin yana cikin zaman dari-dari tun bayan da aka kashe mahaifin hatsabibin dan bindigar.

Rahoton ya kuma bayyana cewa hukumar DSS ta cafke dukkan jami’an CJTF da suka fita aiki a ranar da aka kashe Alhaji Nagode.

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fadi halin da ake ciki bayan sace dalibai a Neja

Sannan, majiyoyin tsaro sun nuna damuwa cewa kisan mahaifin jagoran ’yan bindigan na iya jawo hare-haren ramuwar gayya, musamman kasancewar Fada na da ƙarfi a dazuzzukan yankin.

An ce DSS ta kama dukkan jami'an CJTF da suka fita aikin da ya jawo aka kashe mahaifin dan bindiga a Katsina
Hoton jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, a bakin aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Facebook

Ana fargabar harin ramuwar gayya a Katsina

Majiyoyin tsaron sun kuma bayyana cewa dole ne hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa domin kar lamarin ya tarwatsa sabon sulhun da aka fara ginawa a yankin.

Yayin da ake zaman dari dari a Malumfashi, hukumomi sun yi gargadi ga mazauna yankin su kasance cikin sa ido, su rika sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi da ba a saba gani ba.

Masu fashin baki sun ce dole ne a riƙe yarjejeniyar zaman lafiya da gaskiya da ladabi domin kauce wa sake zubar da jini da tashin tashina.

'Yan bindiga sun sace mata a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mazauna wasu kauyukan Kano sun kwana cikin tashin hankali bayan ’yan bindiga sun kai masu farmaki cikin dare.

'Yan bindigan sun farmaki garuruwan da suka hada da Yan Chibi, Sarmawa da Gano, kuma sun sace mutanen da sun kai takwas, yawancinsu mata ne.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 6 da suka fi ƙoƙari wajen samar da matakan tsaro na kansu

Wani magidanci, Kabiru Usman ya ba da labarin yadda aka sace matarsa, 'yarsa, matar kaninsa da wasu mutanen gari a lokacin wannan hari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com