Hukumar Kwastam Ta Kawo Sabon Tsarin Hana Jami'anta Ta'ammali da Kwaya

Hukumar Kwastam Ta Kawo Sabon Tsarin Hana Jami'anta Ta'ammali da Kwaya

  • Hukumar kwastam ta shirya yaki da matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi daga wajen jami'an da ke aiki a karkashinta
  • Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa ba za su lamunci ma'aikata na aiki a cikin yanayi mara kyau ba
  • Ya bada umarnin gudanar da gwajin miyagun kwayoyi ga sababbin ma'aikata da wadanda ke bakin aiki a halin yanzu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar kwastam ta kasa (NCS), Dr. Bashir Adewale Adeniyi, ya ce za ta fara gwajin miyagun kwayoyi ga jami'anta.

Shugaban na hukumar kwastam ya umarci cewa a rika gudanar da gwajin miyagun kwayoyi ga sababbin ma’aikata da kuma jami’an da ke aiki a yanzu.

Hukumar kwastam za ta yi wa jami'anta gwajin kwaya
Shugaban hukumar kwastam, Dr Bashir Adewale Adeniyi @CustomsNG
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Dr. Adeniyi ya bayyana hakan ne a lokacin rufe taron shugaban hukumar kwastam na shekarar 2025 da aka gudanar a a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku: "Ba a taba jam'iyyar da ta azabtar da 'yan Najeriya kamar APC ba"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kwastam za ta yi gwajin kwaya?

Ya ce wannan mataki na daga cikin gyare-gyaren da ake aiwatarwa domin ƙarfafa gaskiya da ƙwarewa a cikin hukumar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

Hakazalika ya ce matakin zai tabbatar da cewa babu jami’in da ke aiki cikin yanayin da zai iya rage masa hangen nesa ko ya sa ya yi kuskuren da zai zama barazana ga tsaron kasa.

A cewarsa, gwajin miyagun kwayoyi zai zama ɗaya daga cikin matakan tantancewa na karshe ga sabbin ma’aikata kafin a fara horo, yayin da jami’an dake aiki za su rika fuskantar gwaji lokaci zuwa lokaci a matsayin ɓangare na duba lafiyar aiki.

“Sabon umarnin ya fi karkata ga sababbin shigowa, amma jami’an da ke aiki yanzu za su shiga cikin tsarin yayin da muke kan kokarin gina hukuma mara tabon amfani da miyagun kwayoyi gaba ɗaya.”

- Dr. Bashir Adewale Adeniyi

Kwastam ba ta zo da wasa ba

Kara karanta wannan

Gwamnati da 'yan sanda sun yi magana kan harin 'yan ta'adda a makarantar Borno

Adeniyi ya jaddada cewa hukumar ba za ta ƙara lamuntar jami’ai da ke bakin aiki yayin da suke karkashin tasirin miyagun kwayoyi ba.

Ya ce hakan ya zama tilas ne musamman ganin cewa wasu matsalolin da suka taɓa tasowa a wasu hukumar, an gano suna da alaka da amfani da miyagun kwayoyi.

“Ba za mu yi sassauci ba. Za mu tabbatar duk sabon jami’i an gwada shi, domin ba ma son mu rika kashe kuɗin hukuma kan jinyar jami’ai masu fama da shaye-shaye.”

- Dr. Bashir Adewale Adeniyi

Hukumar kwastam za ta rika gwada lafiyar jami'anta
Shugaban hukumar kwastam na duba fareti Hoto: @CustomsNG
Source: Twitter

Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da gwajin a dukkanin ofisoshin hukumar da hedkwata.

Dubban mutane sun nemi aikin kwastam

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kwastam ta kasa (NCS) ta bayyana adadin mutanen da ke neman samun guraben aiki a karkashinta.

Hukumar kwastam ta bayyana cewa ta karɓi takardun masu neman aiki akalla guda 573,523 daga sassa daban-daban na Najeriya.

Ta bayyana cewa ta karbi wannan adadi ne daga masu neman aiki a matakin farko na shirin daukar sababbin ma’aikata da aka fara tun ranar 27 ga Disamba, 2024, wanda aka tallata a jaridu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng