‘Na Kusa Jifansa’: Yadda Obasanjo Ya Batawa Tsohon Gwamna Rai a Taro
- Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Peter Fayose ya tuno bacin rai da ya fuskanta yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa
- Fayose ya ce maganganun Olusegun Obasanjo sun fusata shi ƙwarai a zagayowar haihuwarsa, har ya ji kamar ya buge shi
- Ya ce ya nemi sulhu da Obasanjo kafin bikin amma ya mayar da martani mai cike da zargi da wulakanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fusata shi a taro.
Fayose ya bayyana cewa maganganun Obasanjo a bikin zagayowar haihuwarsa na 65 sun fusata shi matuƙa, har ya ji kamar ya jefe shi.

Source: Twitter
Fayose ya faɗi haka ne a wata sabuwar tattaunawa da ya yi, inda ya bayyana yadda lamarin ya fara tun kafin bikin, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya ce lamarin ya fusata shi har ya ji kamar ya kwace makirufo daga hannunsa ya buge shi.
Abin da ya hada Obasanjo da Fayose
A wurin shagalin a Lagos, Obasanjo ya yi magana kan rikicinsa da Fayose a baya, inda ya ce tsohon gwamnan “ba shi ne mafi nagarta” daga cikin waɗanda ya ba horo ba, duk da cewa ya amince da rawar da ya taka a siyasa.
Fayose ya ce sati biyu kafin bikin, ya yanke shawarar sulhu da mutane da dama da suka yi faɗa a baya, cewar Daily Post.
Ya ce ya samu lambar Obasanjo ne ta hannun abokinsu Osita, sannan ya kira shi domin sulhu, amma ba don neman afuwa ba.

Source: Facebook
Abin da Fayose ya ce game da Obasanjo
A cewarsa, shi bai yi wa Obasanjo laifi ba, illa ma Obasanjo ne ya kifar da gwamnatinsa a lokacin inda ya ce idan akwai wanda ya kamata ya nemi afuwa, to Obasanjo ne.

Kara karanta wannan
Sace dalibai: An taso Tinubu a gaba, malami ya buƙace shi don Allah ya yi murabus
Ya ce Obasanjo ya karɓe shi a gidansa kwanaki kafin bikin, ya kuma tabbatar masa cewa zai halarta duk da wasu ayyuka da yake da su a Rwanda.
A cewar Ayo Fayose, kalaman Obasanjo cike suke da kalamai na wulakanci da zargi, ya yi mamakin yadda za a yi mutum ya faɗi irin wadannan maganganu a lokacin taron zagayowar haihuwar wani.
Amma ya ce ya danne fushinsa saboda mutunci, ba wai saboda shekaru ba, da kuma kasancewar mataimakin shugaban kasa na wurin.
Ya ce:
“Na fusata sosai. Na ji kamar kawai na kwace makirufo na buge shi da shi. Gaskiyar magana kenan.
“Da na san haka za ta faru, me zan yi da Obasanjo? Ina neman takara ne? Ina bukatar yardarsa? A’a.”
'Yadda za a birne ni': Ayodele Fayose
An ji cewa tsohon gwamna Ayodele Fayose ya ba da umarni kan yadda yake son a birne shi bayan ya yi bankwana da duniya.
Fayose ya yi gargadi ga masu zuwa kabarin mutane bayan sun rasu inda ya ce yana son a birne shi cikin makonni huɗu.

Kara karanta wannan
Bidiyon yadda aka wulakanta 'yan kwallon Najeriya a jirgi, an kira su 'yan ta'adda
Shugabanni da dama sun taya shi murna yayin bikin cikar sa 65, ciki har da Gwamna Biodun Oyebanji da ya yaba da gudunmawarsa ga jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
