Abin da Ya Sa Sheikh Gumi Ya Fi Damuwa da 'Yan Bindiga Fiye da Mutanen da Ake Kai Wa Hari

Abin da Ya Sa Sheikh Gumi Ya Fi Damuwa da 'Yan Bindiga Fiye da Mutanen da Ake Kai Wa Hari

  • Sheikh Ahmad Gumi ya kare kansa daga masu zargin cewa ya fi damuwa da 'yan bindiga fiye da mutanen da ake kai wa hare-hare
  • Babban malamin ya bayyana cewa mutane ne ba su fahimce shi ba, amma burinsa a magance matsalar tun daga tushe
  • Dr. Gumi ya ce hukumomin gwamnati na da tsare-tsaren da za su taimaka wa duk wanda harin yan bindiga ya shafa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Babban malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi karin haske kan tattaunawar da yake yi da 'yan bindiga.

Sheikh Gumi, ya ce matsalar tsaron da ke kara ta'azzara a Najeriya, ta na bukatar a shawo kanta tun daga tushe domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Sheikh Ahmad Gumi.
Hoton Sheikh Ahmad Abubakar Gumi a wurin karatu Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Fitaccen malamin ya fadi haka ne yayin da yake jawabi a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin 'Morning Brief' na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi yadda dabararsa ta taimaki gwamnatin Kaduna aka inganta tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ya fi maida hankali kan shawo kan masu kawo hari watau 'yan bindigan da ke aikata ta'addanci fiye da wadanda hare-haren suka shafa.

Sheikh Ahmad Gumi ya kare kansa

Gumi ya ba da misali da likitanci don tabbatar da nufinsa, inda ya ce a duk wani yanayi na gaggawa, mataki na farko shi ne hana ci gaba da barna, ba wai fara jinyar wadanda suka riga suka ji rauni ba.

Ya ce:

"Idan kana da yanayi na gaggawa, abin da ake so ka fara da shi kawai shi ne dakatar da zubar jinin, ba ruwa ka da karayar kashi a farko, ka kula da yadda zuciya ke aiki.”
"Hankalina ya fi karkata ga wadanda ke raunata mutane. Misali wani mahaukaci ya shiga kasuwa da daddare ya rika daba wa mutane da dama wuka, hanyar da zan bi ita ce in kwace wukar daga hannun mahaukacin, ba wai wadanda suka ji rauni ba.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin rashin imani a Kwara

Ahmad Gumi ya jaddada cewa don ya fi damuwa da 'yan bindiga ba yana nufin ya yi watsi da wadanda ake kashewa ko suke samun rauni ba, burinsa shi ne kawo karshen hare-haren gaba daya.

Sheikh Gumi na taimaka wa mutane?

Malamin ya ce bai kai matsayin da zai ba da tallafi kai tsaye ga wadanda matsalar tsaro ta shafa ba, inda ya dage cewa hukumomin Gwamnati da ake da su ne ke da alhakin yin hakan.

"Ni ba wata hukuma ba ce kuma ba zan iya kula da kowa ba. Abin da ya dameni shi ne ya kamata jini ya daina zuba.”
Sheikh Gumi.
Babban malami a Najeriya da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Malamin ya mayar da martani ga masu sukarsa da cewa hanyoyin da yake bi sun fi ba da fifiko ga jin dadin kungiyoyin 'yan bindiga fiye da wadanda abin ya shafa.

Ya dage cewa Gwamnati tana da isassun tsare-tsare don amsa da kula da duka wadanda hare-haren 'yan bindiga ya shafa, kamar yadda Leadership ta kawo.

"Idan kana so ka warkar da cuta, dole ne ka koma baya ka ga likitan halayyar dan adam domin gano me ya haifar da cutar," in ji shi.

Kara karanta wannan

Ahmad Gumi ya bada sharadin tsayawa Nnamdi Kanu a fito da shi daga kurkuku

Shawarar Sheikh Gumi ta taimaka a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce tsaron Kaduna ya inganta da 90% saboda gwamnati ta dauki dabararsa.

Malamin ya danganta saukin matsalar tsaron da yadda gwamnatin Uba Sani ta fara amfani da tsarin tattaunawa da sulhu da miyagun 'yan ta'adda.

Ya jaddada cewa duk wanda ke son a samu zaman lafiya a Najeriya dole ne ya saurari irin wannan tsari na shi, kuma ana ganin amfaninsa a Kaduna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262