Trump: Masana Tsaro Sun Fayyace Gaskiya kan batun Sojojin Amurka Sun Iso Arewa

Trump: Masana Tsaro Sun Fayyace Gaskiya kan batun Sojojin Amurka Sun Iso Arewa

  • An gudanar da bincike game da wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta yana ikirarin cewa sojojin Amurka sun iso Najeriya
  • Haka zalika an gano yadda ake yada bidiyo daga Mali da Burkina Faso ana cewa Najeriya ne domin tada hankalin jama’an kasar
  • Masu sharhi kan lamuran tsaro sun gargadi jama’a su daina yada jita-jita, su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yadawa a intanet

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An bayyana cewa wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa rukuni na farko na sojojin Amurka ya isa jihar Borno karya ne.

Bincike da masana tsaro suka gabatar ya nuna cewa an kirkiri bidiyon karyar ne da amfani da fasahar kirkirarriyar basira wato AI.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, Boko Haram sun guntule kan mata saboda zargin tsafi

Wasu jiragen sojin Amurka
Shugaban Amurka da wasu jiragen sojojin kasar. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sakon da Zagazola Makama ya wallafa a X ya nuna cewa binciken tsaro ya tabbatar cewa bidiyon ba shi da wata alaka da ayyukan soja a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar shi, wannan yunkuri wani sabon salo ne na yada bayanan bogi da ake saka su a intanet domin rikita jama’a da haifar da tsoro.

AI ya hada bidiyon sojojin Amurka a Arewa

Bincike ya tabbatar cewa fasahar AI aka yi amfani da ita wajen kirkirar bidiyon da ake yadawa na cewa sojojin Amurka sun iso Najeriya.

Masana tsaro sun ce babu wani bayani ko rahoto da ke nuna zuwan sojojin Amurka Najeriya kwata-kwata.

Rahotanni sun bayyana cewa ana amfani da irin wadannan bidiyo na bogi wajen ingiza jita-jita da tayar da hankalin jama’a, musamman a lokutan da ake fama da matsalolin tsaro.

Sun yi nuni da cewa fasahohin kirkirar bayanai na kara yawa a lokuta na baya-bayan nan, kuma ya zama wajibi jama’a su yi taka-tsantsan da duk wani abu da suke gani a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

An kama 'dan bindigan da ya gudu Bauchi daga Zamfara da makamai da kudi

Yadda ake yada bidiyon karya a Najeriya

Bincike ya nuna cewa ana yada bidiyon da suka fito daga Mali da Burkina Faso, musamman na yaƙi da ’yan ta’adda, ana cewa a Najeriya ne.

Wani rahoto ya bayyana cewa ana yin hakan ne don a nuna cewa harkokin tsaro sun tabarbare fiye da yadda suke a zahiri.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: The White House
Source: Twitter

An gargadi jama’a da su guji yada irin wadannan rade-radi domin bayanan bogi na iya tayar da tsoro, rikici da kuma rage wa jama’a kwarin gwiwa a kan kokarin da ake yi na tabbatar da tsaro.

Masana tsaro sun kuma gargadi jama’a da su daina yada bayanai marasa tushe da suka taso daga bidiyoyi ko rubuce-rubuce da ba su da tabbas.

An caccaki Obi kan shigowar Amurka Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta caccaki Peter Obi kan wasu kalamai da aka jingina masa.

A wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, an ce Obi ya ce zai goyi bayan Donald Trump ya shigo Najeriya da sojoji.

Kara karanta wannan

Ana maganar Najeriya, an gano yadda Trump ke gallazawa wasu Kiristoci a Amurka

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Najeriya ba za ta manta da maganar Peter Obi ya yi ba a daidai wannan lokaci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng