"Sai an Yi Hakan": Malami Ya Gayawa Shugaba Tinubu Abin da Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro

"Sai an Yi Hakan": Malami Ya Gayawa Shugaba Tinubu Abin da Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro

  • Ana ci gaba da muhawara kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita Najeriya
  • Primate Elijah Babatunde Ayodele ya sanar da Mai girma Bola Tinubu abin da zai kawo karshen matsalar wadda aka dade ana fama da ita
  • Malamin addinin Kiristan ya kuma ba Shugaba Tinubu shawara kan matakan da ya kamata ya dauka don murkushe barazanar 'yan ta'adda

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Primate Ayodele ya gargadi Tinubu cewa matsalar tsaro a Najeriya ba za ta kare ba, muddin gwamnati ba ta ɗauki matakin kama masu karfafawa da ɗaukar nauyin ta’addanci ba.

Primate Ayodee ya ba Tinubu shawara kan rashin tsaro
Primate Elijah Ayodele da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @primateayodele, @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta ce Primate Ayodele ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaransa, Osho Oluwatosin, ya fitar a ranar Talata, 25 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnati da 'yan sanda sun yi magana kan harin 'yan ta'adda a makarantar Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ba za a kawo karshen rashin taaro ba?

Ya ce duk wani ƙoƙari da ake yi yanzu wajen magance rashin tsaro ba zai haifar da da mai ido ba, idan har ba a gano tare da gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci a cikin kasar nan ba.

A cewarsa, ko tallafin da ake samu daga kasashen ketare ba zai yi wani tasiri ba idan har ba a hukunta waɗanda ke daukar nauyin ta'addanci daga cikin gida ba.

“Idan gwamnati ba ta kama waɗanda ke ɗaukar nauyin ta’addanci ba, to ba da gaske take ba, matsalar ba za ta kare ba. Akwai gwamnonin jihohi, manyan sanatoci, da tsofaffin gwamnoni a cikin su."
"Ya kamata a kama su. Idan ba a yi haka ba, to alama ce ba mu da niyyar kawo karshen matsalar.”

- Primate Elijah Ayodele

Primate Ayodele ya dage cewa ci gaba da bada kariya ga manyan mutane da ake zargi suna tallafa wa ayyukan ta’addanci shi ne babban dalilin da ya sa rashin tsaro ke ci gaba da ta’azzara.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya fadi matsalar da ake fuskanta wajen kawar da rashin tsaro

Ya kuma ce ko da Amurka ta saka baki, ba za a ga canji ba sai an hukunta waɗanda ke ba ’yan ta’adda kuɗade.

Primate Ayodele ya ba Tinubu shawara kan rashin tsaro
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele Hoto: Primate Elijah Ayodele
Source: Facebook
“Ko da da taimakon Amurka, idan ba mu gano wadannan mutanen tare da kama su ba, duk kokarin da ake yi zai tafi a iska ne."

- Primate Elijah Ayodele

Ayodele ya ba Shugaba Tinubu shawara

Faston ya kuma shawarci Shugaba Tinubu ya gaggauta amincewa da tsarin ’yan sanda na matakai uku, na jiha, na tarayya da na yankuna — domin karfafa tsaro.

Ya ce kafa irin waɗannan tsarin zai taimaka wajen hanzarta mayar da martani ga barazana a ko’ina cikin kasar.

“Shugaba Tinubu ya amince a ƙirƙiri ’yan sandan jiha, ’yan sandan tarayya, da ’yan sandan yankuna. Wannan zai taimaka wajen rage tsanantar matsalolin tsaro.”

- Primate Elijah Ayodele

Abin da Onanuga ya ce kan 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana dalilin da ya sa sojoji ba za su iya yi wa 'yan bindiga kifa daya kwala ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi halin da ya shiga kan matsalar rashin tsaro a Arewa

Bayo Onanuga ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun san inda 'yan bindiga suke buya a cikin dazuzzuka.

Sai dai, ya nuna cewa ba zai yiwu a kai musu hari ta sama ba saboda gudun kada a hallaka fararen hular da ke hannunsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng