'Yan Bindiga Dauke da Makamai Sun Sake Kai Harin Rashin Imani a Kwara

'Yan Bindiga Dauke da Makamai Sun Sake Kai Harin Rashin Imani a Kwara

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki garin Isapa da ke yankin karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara da yammacin jiya Litinin
  • Wannan hari na zuwa ne awanni 24 bayan mutanen da aka sace a coci a Kwara sun shaki iskar 'yanci, sun koma gida
  • 'Yan bindigan sun nuna rashin tausayi a harin Isapa, inda suka sace mata mai juna biyu da masu shayarwa da kuma kananan yara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Miyagun 'yan bindiga sun sake lai farmaki na rashin tausayi yayin da ake tsaka da murnar kubutar mutanen da aka yi garkuwa da su a harin coci a Kwara.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai sabon hari ne kan mazauna Isapa, wani kauye da ke kusa da Eruku a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.

Kara karanta wannan

"Akwai dalili": Hadimin Tinubu ya fadi abin da ya sa sojoji ba su iya farmakar 'yan bindiga

Jihar Kwara.
Hoton tawirar jihar Kwara a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa 'yan bindigar sun sace akalla mutane 11 a harin, wanda ya daga wa mutane hankali saboda yadda maharan suka tafi da wata mai juna biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ceto wadanda aka sace a coci

Wannan hari na zuwa ne sa'o'i 24 bayan masu ibada, wadanda aka sace suna tsakiyar bauta a coci sun shaki iskar 'yanci.

An ce cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke Ekuru na gudanar da taron godiya don murnar sako masu ibada 18 da aka sace kimanin wata guda da ya wuce.

To sai dai ana cikin wannan taro na godiya ga Allah, kwatsam sai a wasu 'yan bindiga suka shiga cikin cocin suka sace mutane 38 bayan sun harbe uku har lahira.

Mahara sun sace mai ciki a Kwara

Bayanai sun nuna cewa yan bindiga 20 zuwa 30 ne suka kai sabon harin, wanda ya faru da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Katsinawa sun sace iyalan ƴan ta'adda, an tilasta musayar mutanen da aka yi garkuwa da su

An ruwaito cewa sun rika harbi ba kakkautawa yayin da suke gab da shiga, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin gudu don neman tsira, in ji Premium Times.

Wani shugaban al’umma, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a kan sharadin ba za a ambaci sunansa ba, ya ce “an sace mutane goma sha daya (11), bakwai daga cikinsu kuma daga gida daya suke.

"Wadanda abin ya shafa sun hada da mace mai juna biyu, mata masu shayarwa biyu, da kuma yara kanana da dama," in ji shi.
Jami'an 'yan sanda.
Hoton dakarun 'yan sanda su na fareti Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce,

“Eh, mun samu labari, amma ba zan iya cewa komai ba yanzu. Zan shiga Isapa daga Ilorin yanzu. Zan kawo muku karin bayani idan na isa wurin.”

An kama maharan da suka shiga cocin Kwara?

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ‘yn sanda ta karyata bidiyon da ya nuna cewa an kama ‘yan bindigar da suka kai hari tare da sace mutane a wani cocin jihar Kwara.

Ta bayyana cewa labarin da ake yadawa na kama wasu daga cikin ‘yan bindigan da suka kai hari a cocin Christ Apostolic da ke Eruku, a Karamar Hukumar Ekiti, ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

An fitar da cikakken jerin sunayen malamai da daliban da aka sace a jihar Neja

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce babu kamshin gaskiya ko kadan a bayanan da ke cikin bidiyon.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262