Cikin Rashin Imani, Boko Haram Sun Guntule Kan Mata saboda Zargin Tsafi

Cikin Rashin Imani, Boko Haram Sun Guntule Kan Mata saboda Zargin Tsafi

  • Wani tsagin Boko Haram mai biyayya ga Ali Ngulde ya kashe mata biyu a tsaunukan Gwoza bayan zarginsu da yin tsafi
  • An ce an kama matan ne da layu lokacin wani bincike da ‘yan ta’addan suka yi a yankin da suke iko da shi a jihar Borno
  • Tsagin 'yan ta'addan ya ce zai kara tsaurara hukunta mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen asiri ko kokarin tsere musu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Wasu mayakan Boko Haram na bangaren Ali Ngulde sun yanke kan mata biyu bayan zarginsu da aikata sihiri.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe matan bayan sun same su da wasu layu a wuraren da ke karkashin ikon su a tsaunukan Mandara.

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno inda Boko Haram ta yi karfi. Hoto: Legit
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya kara tsananta fargaba a yankin da ake fama da tashe-tashen hankulan da kungiyar ke haddasawa.

Kara karanta wannan

Katsinawa sun sace iyalan ƴan ta'adda, an tilasta musayar mutanen da aka yi garkuwa da su

Boko Haram ta fille kan mata a Borno

Wata majiya ta tabbatar da cewa matan sun fada hannun ‘yan ta’addan ne lokacin da suka gudanar da rangadin bincike a cikin al’ummar da suke iko da ita.

Yayin zagayen da 'yan ta'addan suka yi, sun bayyana cewa duk wanda aka samu da abin da suka kira na “haramun” zai fuskanci hukunci.

Bidiyon da ya bayyana ya nuna yadda aka gurfanar da matan a gaban wani tsarin shari’ar wucin gadi da ‘yan ta’addan ke amfani da shi.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno. Hoto: Dauda Iliya
Source: Twitter

Majiyar ta ce an dauke su daga cikin unguwar zuwa wani lungu na tsaunuka, inda aka yi musu hukuncin kisa don tsoratar da sauran mutane da tilasta bin ka’idojin 'yan Boko Haram.

Majiyar ta shaida cewa:

“Sun ce sun kama matan ne da wasu layu lokacin da suke gudanar da bincike. Suka zargesu da aikata shirka bayan ganin kayayyakin.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jihohin Kebbi da Neja ba, an sace mata a jihar Borno

"Sai suka kai su wani wuri a tsaunukan, inda suka yanke musu kai bayan wannan shari’ar da suka kirkiro.”

Ta kara da cewa an yi wannan kisa ne a gaban wasu mayakan kungiyar da kuma mutanen da suke tsarewa a yankin, don nuna cewa duk wanda ya saba musu zai gamu da hukunci maras sassauci.

Bangaren Ali Ngulde ya kara tsananta hukunci a watannin baya, musamman ga wadanda ake zargi da sihiri, leƙen asiri ko kokarin tserewa daga yankin.

Tsaurara doka da tsaro a Mandara

Masu sharhi kan al’amuran tsaro sun bayyana cewa tsaunukan Mandara sun zama cibiyar tsauraran dokoki da mummunar hukunci ga duk mutanen da suke karkashin ikon Boko Haram.

A bidiyon da suka wallafa, 'yan Boko Haram din sun yi wani bayani da Larabci kafin daga baya su fassara da Hausa.

DSS ta kama wani dan bindiga a Bauchi

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani dan bindiga da ya gudu daga Zamfara zuwa Bauchi ya shiga hannun DSS.

Rahoton da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa dan ta'addan ya koma Bauchi ne yana cewa ya yi hijira saboda hare-hare.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Jami'an DSS sun fara bibiyarsa ne saboda yadda ake ganin yana kashe makudan kudi ba tare da wata sana'ar kirki ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng