EU: Tarayyar Turai Ta Goyi Bayan Farfado da Wasu Kamfanonin Kano

EU: Tarayyar Turai Ta Goyi Bayan Farfado da Wasu Kamfanonin Kano

  • Kungiyar Tarayyar Turai da abokan huldarta sun kaddamar da sabuwar cibiyar kirkire-kirkire ga mata a Kano domin tallafa wa ‘yan kasuwa
  • An ce cibiyar za ta taimaka wajen farfado da tsohuwar masana’antar yadi ta Kano ta hanyar fasaha, kirkire-kirkire da tsarin kasuwanci na zamani
  • Gwamnatin Kano ta goyi bayan shirin tana mai cewa ci gaban mata a fannoni kamar fasahar zamani babbar hanya ce ta gina makomar jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Kungiyar tarayyar Turai (EU) tare da abokan huldarta a Najeriya sun kaddamar da sabuwar cibiyar kirkire-kirkire da fasahar zamani a Kano.

An bayyana cewa cibiyar za ta kasance matattarar horaswa da fasahar zamani ga mata masu kasuwanci.

Wakilan kungiyar tarayyar Turai a Kano
Wakilan EU da wasu mata a jihar Kano. Hoto: New National Star
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa EU ta bayyana cibiyar a matsayin muhimmin mataki na karfafa shigar mata cikin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Amurka ta yi wa Najeriya kan matsalar rashin tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da jiga-jigan taron suka ce

Shugabar Sashen tattalin arziki na ofishin EU a Najeriya da ECOWAS, Inga Stefanowicz, ta yaba da hadin gwiwar da ya ba da damar ganin wannan rana.

Ta ce:

“Kungiyar tarayyar Turai na alfahari da kasancewa cikin masu tallafawa wannan aiki, amma abokan hulda na cikin gida su ne ginshikan farfado da shi.
"Za mu tallafa wa shirin, amma ku — ‘yan kasuwa da al’umma — ku ne za ku tabbatar da cigaban shi.”

Ta kara jaddada jihar Kano a matsayin cibiyar al’adu da tasirin da take samu a fannin fasahar zamani.

Shugabar abokan hulda na Women Venture Studio, Maryam Lawan Gwadabe, ta bayyana cewa nasarar cibiyar ta samo asali ne daga dogon shirin da aka yi.

Tribune ta rahoto cewa ta ce:

“Babu wani abu mai kyau da ke zuwa cikin sauki. Wannan kaddamarwa shaida ce ta juriyar mata da tabbacin cewa matan Arewacin Najeriya na da rawar da za su taka wajen gina tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ra ki bin sahun jihohin da ke kulle makarantu, ta fadi matakin da ta dauka

Ta kara da cewa mayar da hankali kan kirkire-kirkire ya samo asali ne daga tarihin masana’antar yadin Kano.

Ta ce:

“Kano ta taba zama ‘cibiyar hada yadi’ a Afirka ta Yamma. Burinmu shi ne farfado da wannan tarihi ta hanyar fasahar zamani da tsare-tsare.”

Shugaban cibiyar Digital Transformation Centre a Najeriya, Thuweba Diwali, wanda Daniel Ritter ya wakilta, ya bayyana cibiyar a matsayin abu mai muhimmanci ga cigaban tattalin arziki.

Ya ce:

“Mun yaba da jajircewar abokan hulda da suka tsaya tsayin daka har muka kai ga wannan rana.”

Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, ya marabci shirin tare da tabbatar da kudirin gwamnati na bude sababbin hanyoyi ga mata.

Abba Kabir da Aminu Gwarzo
Gwamnan Kano da mataimakinsa a wani taro. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: UGC

Ya kara da cewa gwamnati na aiwatar da shirye-shiryen horas da mata a dukkan kananan hukumomi 44 domin inganta dabarunsu.

Maganar farfado da kamfanonin jihar Kano

Masana’antar yadin Kano ta samo asali tun karni na 15, inda ta shahara a fadin Afirka ta Yamma da kayayyaki masu kyau da zane-zane na hannu.

Kara karanta wannan

Ta ya haka ta kasance: Gwamnatin Kebbi ta gano matsalar da ta auku kafin sace dalibai

Sai dai masana’antar ta fuskanci koma baya saboda kayayyakin da ake shigowa da su, karancin fasaha da kuma rashin masu zuba jari.

Ana sa ran shirin EU na Women Venture Studio da kuma Kano Textile Hub zai farfado da wannan tarihi ta hanyar hada fasahar zamani da kwarewar gargajiya tare da horas da mata.

Abba Kabir ya ba JTF motoci a Kano

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta ba dakarun JTF motoci da babura.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Kano ta ba jami'an tsaro motoci kirar Hilux guda 10 da babura 50 da za su rika aiki da su.

Jami'an tsaron za su yi aiki da motocin ne domin fadada sintiri a wasu yankunan Kano da ke fuskantar barazanar 'yan bindiga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng