Barazanar Tsaro: Gwamnatin Gombe Ta Sanar da Ranar Rufe Makarantu

Barazanar Tsaro: Gwamnatin Gombe Ta Sanar da Ranar Rufe Makarantu

  • Gwamna Inuwa Yahaya ya bada umarnin rufe dukkan makarantu kafin ranar Juma’a saboda tsare-tsaren kare dalibai a jihar
  • Shugaban SUBEB, Dr Esrom Toro, ya ce matakin na da nasaba da karuwar hare-haren makarantu da sace-sacen dalibai a jihohi
  • An umurci dukkan makarantu su kammala jarabawa kafin rufewar, tare da fara sabon bincike na sake farfaɗo da makarantun jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya umurci a rufe dukkan makarantu na jihar zuwa ranar Juma’a, 28, Nuwamba, 2025.

An dauki matakin ne domin kare lafiyar dalibai da malamai sakamakon karuwar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa umarni ya fito ne daga shugaban hukumar SUBEB na jihar, Dr Esrom Toro, wanda ya bayyana matakin a taron da ya gudanar da masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Satar dalibai a Kebbi da Neja, gwamnati ta rufe makarantun da ke iyaka da Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun fargaba a Arewa sakamakon hare-haren makarantu da sace-sacen dalibai a wasu jihohi da ke makwabtaka.

Umarnin rufe makarantu a Gombe

A cikin jawabin nasa, Dr Esrom Toro ya ce umarnin gwamnan ya samo asali ne daga barazanar tsaro da ta shafi kasa baki ɗaya, inda ake samun karuwar hare-haren ‘yan bindiga a makarantu.

Ya bayyana cewa gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci a rufe dukkan makarantun jihar zuwa ranar Juma'a, 28 ga Nuwamban 2025 saboda kare malamai da dalibai.

Ya ce matakin ba dalili ba ne na cewa an firgita, sai dai wani tsari na gaba ɗaya da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a.

Dr Toro ya tabbatar da cewa gwamnati na kan gaba wajen ganin an tsare al’umma daga duk wata barazanar tsaro.

Wata makaranta a jihar Gombe
Makarantar Buhari Estate a Gombe. Hoto: Legit
Source: Original

Umarnin gaggauta jarrabawa a makarantu

Shugaban SUBEB ya umurci dukkan makarantu su tabbatar sun kammala jarabawa kafin ranar Juma’a domin bin umarnin gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ra ki bin sahun jihohin da ke kulle makarantu, ta fadi matakin da ta dauka

Ya ce:

“Za a rubuta jarrabawa daga yau zuwa ranar Juma'a kafin a rufe makarantu, a kammala duk wani abu da ya kamata kafin rufe su.”

Ya ce ba a son dakatar da karatu gaba daya, amma matakin ya zama wajibi ne saboda kare lafiyar al’umma, musamman dalibai da malamai da ke fuskantar barazana a wasu bangarorin kasar.

An kafa kwamati kan makarantun Gombe

A wani bangare na jawabin nasa, Dr Toro ya bayyana cewa hukuma za ta fara sabon aikin tantance makarantun jihar domin inganta su.

Kwamitin da gwamnati ta kafa zai fara gudanar da ziyarce-ziyarcen tantance wasu makarantu a duk faɗin jihar.

Ya jaddada buƙatar duk sakatarorin ilimi na kananan hukumomi su kasance suna da sahihan bayanai game da makarantun da suke kula da su domin baiwa kwamitin damar gudanar da aiki.

Legit ta tattauna da malamin makaranta a Gombe

Wani malamin makaranta a jihar Gombe, Habu Adam Isa ya bayyana cewa sun fara shirin jarrabawa bayan sanarwar.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Bola Tinubu ya dauka bayan sace dalibai a Kebbi da Neja

Ya ce:

"Mun fara shirin jarrabawa. dalibai za su rubuta jarrabawa 4 a rana daya a ranar Laraba. Hakan zai iya tasiri a karatunsu."
"Muna rokon Allah ya kawo mana sauki."

Boko Haram sun sace mata a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da cewa 'yan Boko Haram sun sace wasu mata.

Bayanan da 'yan sanda suka fitar sun nuna cewa an sace matan ne a hanyar su ta dawowa daga gona da yamma.

Dakarun rundunar sun sanar da cewa suna cigaba da bincike kan lamarin tare da cewa suna kokarin ceto matan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng