Gwamnati da 'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Harin 'Yan Ta'adda a Makarantar Borno

Gwamnati da 'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Harin 'Yan Ta'adda a Makarantar Borno

  • An yada jita-jita kan cewa 'yan ta'adda sun kai hari a makarantar Government Girls College da ke birnin Maiduguri na jihar Borno
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta fito da bayyana ainihin abin da ya faru a makarantar da 'yammacin ranar Litinin
  • Hakazalika, gwamnatin jihar Borno ta tura tawaga ta musamman zuwa makarantar domin ganin halin da ake ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta karyata jita-jitar cewa an kai hari wanda ya jawo firgici a makarantar Government Girls College, Maiduguri.

Lamarin ya jawo dalibai sun ruga don neman tsira da yammacin ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamban 2025.

'Yan sanda sun musanta batun harin 'yan ta'adda a makarantar Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno da Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun Hoto: @ProfZulum, @PoliceNG (X)
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce mai magana da yawun rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASP Nahum Kenneth Daso ya bayyana labarin harin da ake yadawa a kafafen sada zumunta a matsayin karya, tare da kira ga jama’a su yi watsi da shi.

Kara karanta wannan

Gwamna Nasir ya gano kuskuren sojoji kan rashin tsaro, ya ba su shawara

Yan sanda sun bayyana dalilin firgicin

Ya ce binciken farko ya nuna cewa firgicin ya samo asali ne daga wata hayaniya da ta tashi tsakanin wasu dalibai da ke kusa da ƙofar gidajen ma’aikata, inda suka ce sun hango wasu mutane da ba su yarda da su ba a bayan katangar makarantar.

Kakakin 'yan sandan ya ce hakan ne ya tada hankula, ya kuma janyo ɗan ƙaramin turmutsutsi, ba tare da an samu rauni ko mutuwa ba.

Ya ce bayan samun kiran gaggawa da misalin karfe 7:30 na dare, tawagar ’yan sanda karkashin jagorancin DCP Garba Audu Bosso ta isa wurin nan take domin tantance abin da ya faru.

“Kwamishinan ’yan sanda na jihar Borno, CP Naziru Abdulmajid, yana kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu su kuma guji yada bayanan da ba a tabbatar da su ba saboda suna haifar da tashin hankali.”

- ASP Kenneth Nahum Daso

Ya tabbatar da cewa kwanciyar hankali ya dawo makarantar, kuma ana ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jihohin Kebbi da Neja ba, an sace mata a jihar Borno

Gwamnati ta karyata labarin harin

A nasa ɓangaren, mai bai wa Gwamna Zulum shawara kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya, ya musanta jita-jitar a shafinsa na Facebook.

Ya ce bayan jita-jitar da ta yadu ta haifar da tsoro, hukumomin tsaro sun garzaya wurin suka kuma dawo da doka da oda.

Gwamnatin Borno ta musanta kai hari a makaranta
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: @ProfZulum
Source: Twitter

Ya ce domin kula da lamarin, gwamnatin jihar ta aika da wakilai zuwa makarantar, ciki har da, kwamishinan ilmi, shi kansa da babban mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai.

“Ana kira jama'a su yi watsi da duk wata karya ko bayanan da ba su da tushe.”

- Dauda Iliya

Gwamna Zulum ya sa ranar Azumi a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi jawabin kai tsaye ga al'ummar jihar.

Gwamna Zulum ya bukaci yan jihar su gudanar da azumi da addu’a a ranar Litinin 24 ga watan Nuwambar 2025 domin neman shiriya daga Allah.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

Hakazalika, ya bada tabbacin cewa gwamnati na ci gaba da aikin farfado da makarantu, asibitoci, kasuwanni da muhimman gine-gine domin tabbatar da cewa kowa ya samu kariya da jin dadin rayuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng