Satar Dalibai a Kebbi da Neja, Gwamnati Ta Rufe Makarantun da Ke Iyaka da Abuja

Satar Dalibai a Kebbi da Neja, Gwamnati Ta Rufe Makarantun da Ke Iyaka da Abuja

  • An rufe makarantu masu zaman kansu da na gwamnati a yankunan da ke kan iyakar Abuja da Niger saboda matsalar tsaro
  • Duk da cewa yankunan ba su fuskanci barazana ba, shugabannin makarantu sun ce sun dauki matakin ne matsayin rigakafi
  • Iyayen dalibai sun samu sako daga makarantu daban-daban da ke bayyana cewa za a tuntube su idan al'amura sun daidaita

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantun kudi da na gwamnati da ke yankunan Madalla, Sabon Wuse, Dakwa da Zuma Rock sakamakon karuwar matsalolin tsaro.

Wannan na zuwa ne bayan sace dalibai da malaman makarantar Katolika ta St. Mary da ke Papiri a jihar Neja, wanda ya sanya gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantu har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ra ki bin sahun jihohin da ke kulle makarantu, ta fadi matakin da ta dauka

Makarantun da ke iyakoki da Abuja sun rufe bayan umarnin gwamnatin Neja
Harabar makarantar gwamnati ta mata da ke Dapchi, inda aka taba sace dalibai. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

An rufe makarantu a iyakokin Abuja

Dakwa, Madalla da Zuma Rock Area garuruwan Neja ne da ke gundumar Dei-Dei, wadanda ke makwabtaka da Abuja in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu malamai sun shaidawa jaridar cewa duk da cewa yankin da suke ba shi da yawan hare-hare, sun yanke shawarar bin umarnin gwamnati domin daukar matakin kariya tun kafin wani abu ya faru.

Malaman sun kara da cewa dalibai sun fara komawa gida tun farkon mako bayan samun sanarwa ta musamman daga gwamnati.

Wasu makarantu ma sun umurci iyaye su zo su kwashe littattafan yaransu domin ci gaba da karatu a gida har sai an sake bude makarantu.

Umarnin gwamnatin Niger ya shafi wasu sassan Abuja

Bincike ya nuna cewa Abuja na kan iyaka da jihohi hudu da ke fuskantar matsalar tsaro — Niger, Kaduna, Nasarawa da Kogi.

Wannan kusancin yana sa wasu yankunan Abuja — musamman Garam da yankunan Bwari da ke daf da Kagarko, Kaduna — shiga cikin matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Hotuna: Bayan harin Kebbi, Neja, iyaye sun kwashe ƴaƴansu daga makarantar Abuja

Saboda haka, mahukunta sun zabi su rufe makarantu da dama bisa umarnin gwamnatin Neja domin kare dalibansu daga duk wata barazana da za ta iya tasowa.

Wannan matakin ya kara tabbatar da yadda barazanar tsaro a jihohin makwabta ke shafar babban birnin kasar, in ji rahoton Trust Radio.

Gwamnatin Niger ta ba da umarnin rufe makarantu bayan sace dalibai
Taswirar jihar Neja da ke makwabtaka da birnin Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Makarantu sun aika sako ga iyayen dalibai

A ranar Lahadi, daya daga cikin makarantun da suka rufe ta aike da sako ga iyaye tana sanar da cewa dalibai za su daina zuwa makaranta nan take.

Makarantar ta kuma jan hankalin iyaye kan cewa kare rayukan dalibai ya fi komai muhimmanci a irin wannan lokaci.

Makarantar ta ce za ta sanar da iyaye ranar da dalibai za su ci gaba da zuwa makaranta idan gwamnati ta tabbatar da dawowar zaman lafiya.

Wannan mataki ya zo ne lokacin da ake shirin gudanar da jarabawar karshen zango, wanda ake tunanin yanzu za a dakatar da shirin har sai na dawo aiki.

Dalibai 50 sun kubuto daga hannun 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dalibai 50 da aka sace a makarantar St. Mary’s Papiri a jihar Neja sun samu nasarar kubutowa daga hannun 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni: Gwamna ya hango hadari, ya rufe dukkan makarantun kwana

Kungiyar CAN ta bayyana cewa har yanzu dalibai 236 da wasu ma’aikata 12 da daliban sakandare 14 na hannun ’yan bindiga.

CAN ta saki sunayen daliban 50 da ta bayyana cewa sun gudo yayin da jami'an tsaro ke kara kaimi wajen ganin an ceto sauran wadanda aka sace.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com