Alkawarin da Amurka Ta Yi Wa Najeriya kan Matsalar Rashin Tsaro

Alkawarin da Amurka Ta Yi Wa Najeriya kan Matsalar Rashin Tsaro

  • Fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan yadda tattaunawa ta kasance tsakanin jami'an gwamnatin Najeriya da takwarorinsu na Amurka
  • Ta bayyana cewa gwamnatin Amurka ta yi alkawura ga Najeriya kan yakin da take yi da matsalar rashin tsaro
  • Hakazalika, ta bayyana cewa kasashen biyu za su yi aiki tare domin shawo kan rikice-rikicen da ake fama da su a kasar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa gwamnatin Amurka ta tabbatar da shirinta na zurfafa haɗin gwiwar tsaro da Najeriya.

Fadar shugaban kasan ta ce Amurka za ta samar da karin kayan leken asiri, kayan yaki da sauran kayan aiki domin karfafa ayyukan yaki da ’yan ta’adda da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a kasar.

Amurka za ta taimakawa Najeriya kan rashin tsaro
Shugaban kasa Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump Hoto: @DOlusegun, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan a shafinsa na X a ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi abin da tawagarta karkashin Ribadu ke yi a Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar Najeriya ta je Amurka

Wannan na zuwa ne bayan taron tattaunawa a makon da ya gabata tsakanin wata babbar tawagar Najeriya da jami’an gwamnatin Amurka, domin ƙarfafa haɗin tsaro da kuma buɗe sababbin hanyoyin aiki tare tsakanin kasashen biyu.

Tawagar da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya jagoranta, ta gana da manyan jami’ai a majalisar dokokin Amurka, ma’aikatar harkokin waje da ma’aikatar yaki.

Wadanda suka shiga cikin tawagar Najeriya sun haɗa da ministan shari'a, Lateef Fagbemi, babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede, Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun da sauransu.

Me suka tattauna a kai?

A cikin sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar, ya ce tattaunawar da aka yi a Washington DC ta bada dama wajen karyata zargin kisan kiyashi a Najeriya.

Ya ce tawagar ta yi bayanin cewa hare-haren ta’addanci na shafar al’ummomi daban-daban ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara canza tunani kan shirin kawo farmaki Najeriya bayan ganawa da Ribadu

Tawagar ta ce kokarin maida matsalar rashin tsro a matsayin rikicin addini ko kabila ba abu ba ne mai kyau, kuma yana iya raba ’yan Najeriya.

“Tattaunawar ta ba da dama wajen gyara kuskuren fahimta game da Najeriya, ta kuma samar da matsaya ta haɗin gwiwa mai ma’ana da Amurka, domin kare al’ummomi masu rauni musamman a yankin Middle Belt."
“Amurka ta kuma nuna shirinta na bayar da karin taimakon jin kai ga al’ummomin da abin ya shafa a Arewa ta tsakiya da kuma tallafin fasaha don karfafa tsarin gano barazana tun kafin ta faru.”

- Bayo Onanuga

Tawagar gwamnatin Najeriya ta je Amurka
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

An amince da kafa kwamiti na hadin gwiwa

A cewar fadar shugaban kasa, kasashen biyu sun amince su fara aiki nan take da tsarin haɗin gwiwa, tare da kafa kwamiti na musamman domin daidaita duk matakan tsaro da aka amince a kansu.

Onanuga ya kara da cewa tawagar Najeriya ta sake tabbatar da kudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na karfafa matakan kare fararen hula.

“Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tana da cikakkiyar masaniya kan yadda ake da matukar damuwa game da ’yancin addini da tsaro a kasa, kuma tana tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ana ɗaukar matakai cikin gaggawa domin kare kasar."

Kara karanta wannan

Muhawara ta raba 'yan majalisar Amurka 2 kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya

- Bayo Onanuga

Amurka ta yi Allah wadai da sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta yi magana kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihohin Neja da Kebbi.

Gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da harin inda bukaci a gaggauta ceto daliban daga hannun tsagerun 'yan bindiga.

Hakazalika, ta bayyana cewa dole ne gwamnatin Najeriya ta dauki matakin kare yankunan da ke fuskantar barazana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng