Kwana Ya Kare: Tsohon Hadimin Gwamna kuma 'Dan Jarida, AbdulLateef Ya Rasu
- Babban dan jarida kuma tsohon hadimin gwamnan jihar Legas, Bayo Osiyemi ya rasu yana da shekaru 75 da haihuwa
- Iyalansa sun tabbatar da cewa Osiyemi, wanda asalin sunansa shi ne AbdulLateef ya rasu da safiyar yau Litinin, 24 ga watan Nuwamba, 2025
- Marigayin ya rike mukamai da dama a gwamnatin jihar Legas da kuma aikin jarida kafin ya koma ga mahaliccinsa a yau
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Prince Bayo Osiyemi, tsohon Babban Sakataren Watsa Labarai na gwamnan farko na jihar Legas a mulkin farar hula, Alhaji Lateef Jakande, ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin wanda aka fi saninsa da lakabin “Charming Prince”, ya rasu yana da shekaru 75 da haihuwa a duniya.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Osiyemi ya rasu ne a ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da rasuwar Prince Osiyemi
A cikin wata sanarwar da iyalinsa suka fitar, wacce Seyi Osiyemi ya sanya wa hannu a ranar Litinin, ta ce:
“Cikin bakin ciki da alhini mai zurfi muke sanar da rasuwar mahaifinmu, mijinmu, kakanmu, kuma jagora a cikin al’umma mai daraja, Prince Bayo Osiyemi.
“Ya rasu da safiyar yau, 24 ga Nuwamba, 2025. Yayin da muke cikin zafin rasa shi, muna kuma murna da irin rayuwa mai kyau kuma ta kirki da ya yi tare da yan uwa da abokan arziki.
“Za mu sanar da cikakkun bayanai game da bikin tunawa da shirye-shiryen jana’iza a nan gaba. Allah Ya jikansa da rahama.”
Mukaman da ya rike a gwamnati da gidan jarida
Osiyemi ya taɓa rike mukamin Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Masarautu a lokacin gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta jihar Legas.
Haka kuma ya taɓa zama Shugaban Karamar Hukumar Mushin, sannan ya yi aiki a matsayin editan jaridar Lagos News, kuma ya taba rike shugabancin Penby Communications.
Marigayi tsohon hadimin gwamnan ya kasance marubuci mai sharhi a jaridar The Nation ta mako-mako.
Takaitattun bayani game da Osiyemi
An haifi Prince Osiyemi ne a ranar 4 ga Fabrairu, 1950, a cikin iyalan Sisu da Arowosugbo na Ijebu Igbo, garin da ya fi girma a jihar Ogun.
Ya gaji sarauta ne daga ɓangaren mahaifiyarsa, wacce ta fito daga gidan sarautar Arowosugbo a jihar Ogun.

Source: Facebook
An haife shi a gidan mabiya addinin Musulunci kuma suka rada masa suna Abdul-Lateef, kamar yadda Leadership ta kawo.
Sunansa na gargajiya, Omopeninu (jaririn da ya daɗe a cikin mahaifa), yana nuni da jinkirin haihuwarsa wanda ake cewa ya kai shekaru uku da watanni huɗu kafin a haife shi.
Babban dan jarida, Agbese ya mutu
A wani rahoton, kun ji cewa daya daga cikin fitattun ’yan jarida kuma mamallakin jaridar Newswatch, Dan Agbese, ya rasu yana da shekara 81.
Agbese ya shahara wajen rubuce-rubuce masu tasiri kuma ya shafe shekaru masu ɗimbin yawa yana ba da gudunmawa a aikin jarida tun daga 1980.
Ana ganin dai rasuwarsa za ta bar babban gibi a harkar jarida, musamman ga waɗanda suka san shi a matsayin jagora, jajirtaccen edita da ya ba da gagarumar gudunmawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


