Gwamna Nasir Ya Gano Kuskuren Sojoji kan Rashin Tsaro, Ya Ba Su Shawara

Gwamna Nasir Ya Gano Kuskuren Sojoji kan Rashin Tsaro, Ya Ba Su Shawara

  • Gwamnan jihar Kebbi ya sake nuna damuwarsa kan yadda sojoji suka janye kafin dalibai mata a makarantar GGCSS Maga
  • Nasir Idris ya yi kiran da a binciki dalilin da ya sanya aka janye dakarun sojojin 'yan mintuna kadan kafin 'yan bindiga su kawo harin
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa da sun san za a janye sojojin da sun rufe makarantar domin hana aukuwar harin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi muhimmin kira ga rundunar sojoji kan yakin da take yi da matsalar rashin tsaro.

Gwamna Nasir Idris ya bukaci rundunar sojojin da ta canja dabarar da take amfani da ita wajen yaki da matsalar tsaro a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan Kebbi ya koka kan rashin tsaro
Babban hafsan tsaro, Olufemi Oluyede da Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: @NigerianArmyInfo, @NasirIdrisKIG
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Nasir ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin lokacin da ya karɓi bakuncin shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, a fadar gwamnati da ke Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya sanya ranar fara azumi, addu'o'i, ya shawarci Musulmi, Kirista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Nasir ya ce kan sojoji?

Gwamnan ya sake nanata bukatarsa ta a binciki dalilin da ya sa aka janye sojojin da aka tura zuwa makarantar Government Comprehensive Girls Secondary School, Maga, mintuna kaɗan kafin ’yan bindiga su sace dalibai 25.

“Ta ya ya za a ce ’yan bindiga sama da 500 na yawo a babura kan manyan hanyoyinmu ba tare da an dakatar da su ba?"
"Mun sauke nauyin hukumomin tsaro da ke kanmu. Mun samar da kayan aiki, mun sayo musu motocin ​ fiye da 100, amma tsarin tsaron su bai aiki.”
“Da mun san za su bar ’ya'yan mu ga ’yan bindiga, da ba mu saurari shawararsu ta tura jami’ai ba. Da kawai mun rufe makarantar.”

- Gwamna Nasir Idris

Gwamna Idris ya kara da cewa akwai yiwuwar wasu makiya na ciki da wajen gwamnati na kokarin kawo cikas ga gwamnatin jihar da ta tarayya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dauki mataki kan dakaru da ake zargi sun janye kafin sace daliban Kebbi

“Kullum ana kai hare-hare. Jiya Kebbi, yau Niger da Kwara. Wa ya san wane yanki za a kai hari gobe? Dole mu dakile wannan matsalar tsaro gaba ɗaya.”

- Gwamna Nasir Idris

Gwamna Nasir Idris ya tabo batun rashin tsaro
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Shugaban majalisa ya bada tallafi

A nasa bangaren, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce ziyarar da suka kai Kebbi, sun kai ta ne domin jajantawa al’ummar jihar kan sace dalibai da kuma kisan mataimakin shugaban makarantar da mai gadin makarantar.

Ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 30 ga iyalan mataimakin shugaban makarantar da mai gadin da suka rasa rayukansu.

Tajudeen Abbas ya bukaci gwamnan da ya sake wa makarantar suna domin girmama jarumtar mataimakin shugaban makarantar wanda ya mutu yana kare dalibai.

“Muna tare da ku, kuma za mu ci gaba da neman hanyar ganin an ceto ’yan matan cikin koshin lafiya.”

- Tajudeen Abbas

Gwamnatin jihar Kebbi a kan ceto dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatn jihar Kebbi ta bada tabbacin cewa za a kubutar da daliban makarantar GGCSS da 'yan bindiga suka sace.

Hadimin Gwamna Nasir Idris a kan yaɗa labarai, Yahaya Sarki, ya bayyana cewa jami'an tsaro suna aiki ba dare ba rana.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Majalisar dinkin duniya ta shiga lamarin sace dalibai a Neja

Yahaya Sarki ya kara cewa an ɗauki matakan da za su tabbatar da cewa an kuɓuto da yaran daga hannun miyagun 'yan bindigan da suka yi garkuwa da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng