Musa: Tsohon Hafsan Tsaro Ya Bayyana Wadanda Za Su Iya Magance Rashin Tsaro a Najeriya
- Tsohon babban hafsan tsaro na kasa (CDS), Janar Christopher Musa, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro
- Janar Christopher Musa ya bayyana cewa 'yan kasashen waje ba za su iya warware matsalar rashin tsaro ba
- Ya bukaci 'yan Najeriya da su kasance 'yan uwan juna ka da su bari rarrabuwar kawuna ta shigo tsakaninsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon babban hafsan tsaro na kasa (CDS), Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.
Christopher Musa ya bayyana cewa ’yan kasashen waje ba za su warware matsalar tsaro ta Najeriya ba, yana mai jaddada cewa ’yan Najeriya ne kawai za su iya ceto kasar.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce Janar C.G Musa ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi yayin taron al’adu da kungiyar tsofaffin daliban makarantun sakandire na gwamnatin tarayya (USOSA) ta shirya a Abuja.
An shirya taron ne domin nuna al’adun Najeriya da kuma karfafa haɗin kan kasa.
Janar Christopher Musa ya yi jawabi
Janar Christopher Musa ya ce al’adun da aka gabatar ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya na iya rayuwa tare cikin haɗin kai, duk da bambancin kabila da addini.
“Abin da mu ke gani yau shi ne yadda Najeriya take a dunkule waje ɗaya, domin zama tsintsiya madaurinki daya."
"Duk da bambancin al’adu, addinai da al’ummomi, mun taru a nan tare. Hakan shi ne yadda ya kamata Najeriya ta kasance.”
- Janar Christopher Musa
Ya roki ’yan Najeriya da su guji rarrabuwar kawuna, su kuma hadu waje daya domin gina kasa tare.
“Dole mu koyi rayuwa tare. Mu koyi kaunar juna. Mu koyi kaunar kasarmu. Ba wanda zai yi mana haka face mu da kanmu.”
- Janar Christopher Musa
Me ya ce kan barazanar Trump?
Da aka tambaye shi game da barazanar Shugaban Amurka, Donald Trump, na amfani da karfin soji a Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce:

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka, Trump ya kara daukar zafi, ya kira Najeriya da kalma mara dadin ji
“Babu wanda zai ceci ƙasarmu face mu. Mu ne za mu yi, kuma muna da ikon yin hakan.”
A nasa bangaren, shugaban USOSA na kasa, Michael Magaji, ya ce kungiyar na ɗauke da nauyin tarihi na kare haɗin kan Najeriya da bunkasa zaman tare.
“USOSA tana da nauyi a kanta wajen tallafa wa haɗin kai a cikin bambance-bambancenmu, tare da wanzar da zaman lafiya da hakuri a ƙasa.”
- Michael Magaji

Source: Facebook
Magaji ya tunatar da cewa an kafa makarantun sakandire na gwamnatin tarayya ne bayan samun ’yancin kai domin haɗa matasa daga dukkan yankunan Najeriya a wuri guda, domin samar da fahimta, kwarewa da shugabanci.
“Shekaru 50 zuwa 60 da suka gabata, lokacin da aka kafa makarantun sakandiren gwamnatin tarayya, an yi hakan ne domin samar da wani wuri da matasan Najeriya daga ko ina za su haɗu su gina kasa tare."
- Michael Magaji
Sojoji sun gano maboyar 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ci karo da maboyar 'yan ta'adda a yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
"Babu wurin zaman ƴan ta'adda a Kebbi": Gwamnati ta fadi yadda aka kai hari makaranta
Sojojin sun ci karo da maboyar 'yan ta'addan ne a kokarin da suke yi na ceto daliban da aka sace a jihar Neja.
Dakarun sojoji daga FOB Gulbin Boka sun yi wa ’yan ta’adda kwanton-bauna yayin da suke kokarin haduwa da wasu abokansu a kusa da Magaman Daji a karamar hukumar Mariga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
