Gwamnatin Zamfara Ta Ki Bin Sahun Jihohin da Ke Kulle Makarantu, Ta Fadi Matakin da Ta Dauka

Gwamnatin Zamfara Ta Ki Bin Sahun Jihohin da Ke Kulle Makarantu, Ta Fadi Matakin da Ta Dauka

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta saba da wasu gwamnatocin jihohin Arewa da ke kulle makarantu saboda matsalar rashin tsaro
  • Kwamishinan ilmi na jihar ya bayyana cewa ba za su kulle makarantu ba domin akwai matakan da suka dauka don tabbatar da tsaro
  • Ya bayyana cewa gwamnati ta yi duk abubuwan da suka kamata domin ganin cewa an ci gaba da yin karatu a makarantu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta da niyyar rufe makarantu, duk da yawaitar matsalolin tsaro da sace dalibai da ake fuskanta a wasu jihohin Arewacin kasar.

Maimaikon haka, gwamnatin ta ce ta kaddamar da karin matakan tsaro domin kare makarantun jihar tare da tabbatar da cewa dalibai na ci gaba da zuwa aji cikin kwanciyar hankali.

Gwamnatin Zamfara ba za ta rufe makarantu ba
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare Hoto: Dauda Lawal
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha na jihar, Wadatau Madawaki, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a wani taron da kungiyar daliban jihar Zamfara ta shirya a Gusau.

Kara karanta wannan

Ta kacame tsakanin gwamnatin Kebbi da Sanata kan matsalar tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanansa na zuwa ne a daidai lokacin da aka sace dalibai 25 na makarantar Government Comprehensive Secondary School, Maga, a jihar Kebbi, da kuma sace dalibai da malamai 315 a St. Mary’s Catholic School, jihar Neja.

Ba za a rufe makarantu a Zamfara ba

Wadannan hare-hare sun sa wasu jihohi a Arewa su rufe makarantunsu gaba ɗaya, amma Zamfara ta ce ba za ta bi sahun su ba.

Kwamishinan ya bayyana cewa sun riga sun dauki dukkanin matakan da ya kamata su dauka.

"Mun riga mun ɗauki matakan da ya kamata mu ɗauka. A harkar tsaro ba a bayyana komai ga kafafen watsa labarai, amma mun ɗauki duk matakan da suka dace don kare dalibanmu."
"An kula sosai da tsaron makarantunmu da yaranmu."

- Wadatau Madawaki

Ya kara da cewa suna aiki tare da dukkan hukumomin tsaro, waɗanda ke ba su goyon baya wajen tabbatar da makarantu na ci gaba da aiki ba tare da wani tsaiko ba.

Kara karanta wannan

Hotuna: Bayan harin Kebbi, Neja, iyaye sun kwashe ƴaƴansu daga makarantar Abuja

“Muna da tabbacin cewa komai zai tafi lafiya, kuma harkar ilmi za ta ci gaba har larshen zangon karatu."

- Wadatau Madawaki

Dalilin kin rufe makarantun jihar Zamfara

Madawaki ya bayyana cewa jihohin da suka rufe makarantu suna da na kwana, inda dalibai ke kwana a makaranta, kuma yawanci ’yan bindiga suna kai hare-hare ne da daddare.

“A Zamfara ba mu sake bude tsarin makarantun kwana ba saboda tsaro. Makarantunmu na rana ne kawai. Wannan ya sa ba mu ga dalilin da zai sa mu rufe su gaba ɗaya ba."

- Wadatau Madawaki

An rufe wasu makarantun

Kwamishinan ya ce a makarantu sun riga sun kasance a rufe a yankunan da ake fama da matsalar tsaro sosai.

“Inda muka ga cewa tsaro ba shi da tabbas, mun riga mun rufe makarantu. Inda kuma akwai zaman lafiya, dalibai sun ci gaba da karatu saboda zangon karatu yana dab da karewa."

- Wadatau Madawaki

Gwamnatin Zamfara ta fadi dalilin kin rufe makarantu
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara Hoto: Mugira Yusuf
Source: Facebook

Za a tsawaita hutun manyan makarantu

Kwamishinan ya kara da cewa wasu manyan makarantu, ciki har da jami’ar jihar, kwalejin fasaha da kwalejin ilmi, sun riga sun tafi hutun karshen shekara.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnatin Kebbi ta dauki mataki kan makarantu bayan sace dalibai

“Ya kamata su dawo a watan Disamba, amma saboda suna da ɗalibai masu kwana, mun tsawaita hutunsu zuwa watan Janairu domin tantance yanayin tsaro kafin su koma."

- Wadatau Madawaki

Zamfara ta yi wa marayu auren gata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta shirya gudanar da auren gata ga marayu.

Gwamnatin ta hannun hukumar Zakka da Wakafi ta bayyana cewa za ta aurar da marayu guda 200 a fadin jihar.

Hakazalika, hukumar za ta ba wa mata 200 da ke gudanar da kananan sana’o’i tallafin jari domin inganta rayuwarsu da faɗaɗa harkokin kasuwancinsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng